Sojin Sama Sun Murkushe Mayakan Boko Haram 30, Kwamandoji 3 Tare da Jikkata Wasu 40 a Borno

Sojin Sama Sun Murkushe Mayakan Boko Haram 30, Kwamandoji 3 Tare da Jikkata Wasu 40 a Borno

  • Jiragen yakin sojojin saman Najeriya biyu sun kai hare-harea kan kungiyar ta'addanci na Boko Haram
  • Dakarun rundunar sojin NAF sun kashe mayakan Boko Haram 30 da kwamandojinsu uku tare da jikkata wasu 40 a jihar Borno
  • Kafin nan, an yi kazamin hari tsakanin bangarorin Boko Haram da ISWAP wanda ya kai ka halaka wasu mayaka

Borno - Hare-haren da jiragen yakin sojojin Najeriya biyu suka kaddamar ya murkushe mayakan Boko Haram 30 ciki harda kwamandoji uku a dajin Sambisa.

An kashe yan ta'addan ne a ranar 1 ga watan Janairu, bayan jirgin NAF ya yi yayyafin bama-bamai a sansanoninsu hudu da suka hada da Bula Jitoye, Halka Kojoye da Halka Alai, Bulamaye a karamar hukumar Bama.

Jihar Borno
Sojin Sama Sun Murkushe Mayakan Boko Haram 30, Kwamandoji 3 Tare da Jikkata Wasu 40 a Borno Hoto: The Cable
Asali: UGC

An yi karo tsakanin Boko Haram da ISWAP

Zagazola Makama, ya saki wani bidiyo inda aka gano mayakan na Boko Haram kan babura, suna kona gidaje da ababen hawa da kuma kashe wasu yan tsirarun mambobin ISWAP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakan ya faru ne awanni 24 da suka shige, bayan wasu zazzafan hare-hare da suka gudana tsakanin ISWAP da Boko Haram a yankunan TOUMBUN ALLURA da KANGAR.

Ali Ngulde da sauran manyan kwamadoji da suka hada da Abu Nazir, Muke, Ba'a Isa, da Mallam Abubakar ne suka jagorancio munanan hare-haren.

Majiyoyin sun bayyana cewa shiryayyen harin ta sama da kasa na zuwa ne yan awanni bayan karon da yan ta'addan suka yi a cikin yankin gaba daya.

Jiragen yaki sun kashe mana mayaka 30 da kwamandoji uku, dan Boko Haram

Har ila yau, majiyoyin sun bayyana cewa harin sojin sama ya kashe daya daga cikin kwamandojin mai suna Kyaftin ko likita a sansanin Bula Jitoye.

Ya kuma bayyana cewa sauran kwamandojin biyu da ba a bayyana sunayensu ba sun mutu ne a Halka Kojoye da Halka Alai.

A cewar majiyoyin, an jiyo daya daga cikin yan ta'addan yana cewa:

"Muna kashe mayakan ISWAP sannan muna kwace dukkanin makamansu. Amma babban matsalarmu shine cewa jirage na kashemu muma.
"A ranar 1 ga watan Janairu, mun rasa kimanin mayaka 30 harda kwamandojinmu uku, harma da likita an kashe shi a harin. Muna sonyakarsu amma muna tsoron jirgin."

An murkushe Shugaban ’Yan Bindiga a Katsina, Sun Kwato Alburusai da Kudade

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da murkushe kasurgumin dan bindiga bayan kai wani babban hari kan jami’an tsaro a jihar.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar,Gambo Isah, kakakin rundunar ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 2 ga watan Janairun 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel