Matasa Yan Kishin Kasa Sunyi Gargadi Mai Karfi Ga Obasanjo Kan Goyon Bayan Peter Obi

Matasa Yan Kishin Kasa Sunyi Gargadi Mai Karfi Ga Obasanjo Kan Goyon Bayan Peter Obi

  • An gargadi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya dena fada wa yan Najeriya abinda za su yi, musamman matasa wanda za su zaba a matsayin shugaban kasa a 2023
  • Kungiyar matasa masu kishin kasa na Patriotic Youth Front of Nigeria (PYFN) ce ta yi wannan gargadin a ranar Talata 3 ga watan Disamba
  • A cewar PYFN, Obasanjo ba shi da hurumin fada wa yan Najeriya su zabi Peter Obi gabanin babban zaben 2023

Kungiyar matasa masu kishin kasa na Patriotic Youth Front of Nigeria (PYFN) ta yi watsi da kakabawa matasan Najeriya dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour.

Biyo bayan mara wa Peter Obi baya da tsohon shugaban kasar ya yi a baya-bayan nan, kungiyar ta ce Obasanjo bai cancani ya bawa matasan Najeriya shawara ba, rahoton Legit.ng

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Bayan Obasanjo, Wani Babban Jigo a Najeriya Ya Sake Goyon Bayan Takarar Obi

Obasanjo da Peter Obi
Matasa Yan Kishin Kasa Sunyi Gargadi Mai Karfi Ga Obasanjo Kan Goyon Bayan Peter Obi. Hoto: Peter Obi
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tsohon shugaban kasar a budadiyar wasika da ta aike wa matasan Najeriya a ranar Lahadi, ya bukaci su zabi Peter Obi wanda ya bayyana a matsayin, 'wanda ke daukan shawara a wurinsa'.

Amma PYFN cikin sanarwar manema labarai da ta fitar a ranar Talata, 3 ga watan Disamba, ta hannun shugabanta, Maxwell Ogar, ta ce "shi kansa Obasanjon yana da laifukansa don haka ba shi ya dace ya shawarci matasan Najeriya kan wanda za su zaba ba."

Kungiyar ta bayyana tsohon shugaban kasar a matsayin daya cikin wadanda suka yi sanadin kallubalen - tattalin arziki, tsaro, da siyasa a kasar 'amma yana kokarin canja tarihi' ya gabatar da kansa a matsayin jarumi kuma a zahiri ba hakan bane.

Ta daga cewa 'marawa Peter Obi baya da Obasanjo ya yi matsala ne ga dan siyasan kasar da ke tasowa domin akwai hujja da ke nuna duk abin da Obasanjo ya sa hannunsa yana lalacewa ne.'

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada A Ji Ya Jinjinawa Obasanjo Kan Goyon Bayan Peter Obi a 2023

Matasan sun nuna fushinsu kan goyon bayan na Obasanjo

Goyon bayan tafiyar ta Obidient ya janyo rashin sa'a ne ga takarar shugaban kasa na Peter Obi.

Ogar ya ce:

"Mun lura ya zama dole mu ja kunnen tsohon shugaban kasa Obasanjo saboda kokarin yaudaran yan Najeriya kan ainihin halinsa.
"Obasanjon da ya yaga katinsa na PDP ya kuma yi rantsuwa ya dena siyasar jam'iyya, yanzu ya nada kansa shugaban jam'iyyar Labour.
"Shin ko Obasanjo bai san wariyar addini da kabilanci da Peter Obi ya yi bane ta hanyar kyautatawa yan darikar katolika zalla da yan kabilansa a matsayin gwamnan Anambra.
"Idan Obasanjo bai san wannan mumunan halin da 'yaronsa' ba, tabbas ba zai ce bai da masaniya kan takardun tonon silili na Pandora Papers ba, inda aka ga yadda Peter Obi ya saka kudin gwamnati a kasuwancin yan uwansa. Wannan abin ya sha banban da abin da matasa ne nema."

Kara karanta wannan

Fadar Bauhari ga Obasanjo: Tarihin da Buhari ya Kafa Har ka Mutu ba Za ka Iya Ba

Gwamna Ortom ya yabi Obasanjo kan goyon bayan Peter Obi

A wani rahoton, gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya jinjinawa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan goyon bayan dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi.

Ortom ya bayyana cewa idan ba domin ba jam'iyyarsu daya da Obi ba, da shine zai jagoranci yakin neman zabensa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel