Saura Makonni 7 Zabe, Kwankwaso Ya Shirya Gadan-Gadan, Ya Nada Kwamitin Takara

Saura Makonni 7 Zabe, Kwankwaso Ya Shirya Gadan-Gadan, Ya Nada Kwamitin Takara

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya amince da kwamitin da zai taya shi yakin zama shugaban Najeriya a NNPP
  • Jam’iyyar ta fitar da sunayen ‘yan kwamitin neman takarar yayin da shirye-shiryen takara suka yi nisa sosai
  • ‘Yan kwamitin sun hada da jagororin NNPP, ‘yan takararta da ‘yan majalisar tarayya da na dokokin jihohi

Abuja - A ranar Talata, 3 ga watan Junairu 2023, jam’iyyar NNPP ta nada kwamitin da zai yi mata aikin yakin neman zaben shugaban kasa a Najeriya.

Ibrahim Adam, wani hadimin ‘dan siyasar ya fitar da sunayen ‘yan kwamitin neman takarar Rabiu Musa Kwankwaso a karkashin jam’iyyar hamayyar.

Kamar yadda ya bayyana a shafukansa na Twitter da Facebook, Malam Ibrahim Adam ya ce an nada shi ya jagoranci sashen gudanarwa ne na kamfe.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Khadijat, Matashiyar Da Ta Nemi Takarar Shugaban Kasa Ta Samu Babban Mukami a PCC

Legit.ng Hausa Rabiu Kwankwaso ya amince da ‘yan kwamitin da aka zakulo, kuma za a rantsar da ‘yan kwamitin ne a ranar 9 ga watan Junairun nan.

Sanarwar ta ce za a yi bikin rantsarwar ne a dakin taron A-Class da ke titin Kashim Ibrahim a unguwar Wuse a birnin tarayya Abuja da karfe 11:00 na safe.

Yadda aka tsara kwamitin PCC

Babban kwamitin yana kunshe da shugabanni, majalisar masu bada shawara da kananan kwamitoci. Madam Folashade Aliu za ta jagoranci tafiyar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso wajen bude ofishin NNPP Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Sakararen NNPP na kasa, Dipo Olayoku ya bada wannan sanarwa a madadin jam’iyya da ‘dan takarar.

Rabiu Kwankwaso ne shugaban kwamitin, sai Isaac Idahosa da Farfesa Rufai Ahmad Alkali za su zama mataimakansa, Folashade Aliu kuma sakatariya.

Dr. Boniface Aneibonam shi ne shugaban BOT, sai Mashood Asiwaju Shittu da Taofik A. Adeleke za su zama shugabanni a shiyyoyin Arewa da na Kudu.

Kara karanta wannan

2023: Abin da ya sa Mu ka Tsaida Bola Tinubu a Jam’iyyar APC Inji Sanatan Arewa

Sauran 'yan kwamitin

A kwamitin akwai jagorori na sashen dabaru, tsare-tsare, walwala, ICT, tsaro, harkar matasa, dalibai da mata, sarakuna da malamai da magoya baya.

Kwamitin PCC yana dauke daukacin ‘yan majalisar NEC na NNPP, ‘yan takarar Gwamnoni, da jagororin yakin neman zaben shugaban kasa a jihohi.

Sauran ‘yan kwamitin sun hada da ‘yan majalisar BOT, tsofaffin ‘yan majalisa ko masu-ci da shugabannin majalisun dokoki da wasu da aka zakulo.

Kwankwaso ya samu yabon Shettima

Kun ji labari ‘Dan takaran mataimakin shugaban kasa na Jam’iyyar APC a 2023, Kashim Shettima ya yabi Rabiu Kwankwaso da aka yi hira da shi.

Sanata Kashim Shettima ya yabi abokin gabansu na NNPP, amma ya soki Alhaji Atiku Abubakar da Peter Obi da suke neman takara a PDP da LP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel