Shettima Ya Yabi Kwankwaso, Amma Ya Kwankwashi Kan Atiku da Peter Obi a Bidiyo
- Barista Audu Bulama Bukarti sun tattauna da Kashim Shettima a shirin fashin baki a Facebook
- A hirar ne Kashim Shettima ya yabi Rabiu Kwankwaso, amma ya soki sauran abokan takaransu
- ‘Dan takaran mataimakin shugaban kasan na APC ya yi habaici ga Atiku Abubakar da Peter Obi
Kano - A ranar Lahadi, 1 ga watan Junairu 2023 aka yi hira ta musamman da Kashim Shettima wanda shi ne ‘dan takaran mataimakin shugaban kasa a APC.
Legit.ng Hausa ta fahimci an zanta da Sanata Kashim Shettima ne a wani sabon shiri na fashin baki wanda su Barista Audu Bulama Bukarti suka shigo da shi.
Kashim Shettima shi ne bako na farko da aka yi hira da shi a wannan shiri a dandalin sada zumunta, a nan ne ya yi bayanin cancantar Bola Tinubu.
Baya ga Bulama Bukarti, shahararrun ‘yan jaridar nan da kuma lauya, Jaafar Jaafar da Abba Hikima sun bada gudumuwarsu a wannan hirar da aka shirya.
Shettima ba zai taba Kwankwaso ba
An tsakuro bangaren tattaunawar nan a Twitter, inda aka ji Shettima yana kwararo yabo ga daya daga cikin abokin hamayyarsu, Rabiu Musa Kwankwaso.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da aka bijiro masa da maganar sauran ‘yan takara, Sanatan na Borno ta tsakiya ya ce Rabiu Kwankwaso mutumin kirki ne, don haka ba zai iya sukar shi ba.
‘Dan siyasar ya ce a lokacin da ya rike Gwamna a jihar Kano, Sanata Kwankwaso ya yi aiki, sannan kuma ya gina al’umma, akasin sauran masu neman mulki.
Kwankwaso ya gina mutane, sauran fa?
“Ba zan ce Rabiu Musa Kwankwaso mutumin banza ba ne, ba zan zagi Kwankwaso ba.
Kwankwaso ya yi aiki a Gwamnan Kano, tsakani da Allah fa nake fada maka, amma ka je wasu wuraren ka gani.
Su wa suka gina? Wa suka rena?
Wani ya yi mataimakin shugaban kasa, ya yi wanene…ka kirga mutane uku da suka rena, suka maida su wani abu?
Wani don yana saida giya kurum ba zai sa ya zama ya cancanta ya zama shugaban kasar Najeriya ba.
- Kashim Shettima
Bisa dukkan alamu Kashim Shettima yana habaici ne ga Atiku Abubakar da Peter Obi, inda ya dage a kan cewa Tinubu ya fi cancanta ya rike Najeriya a 2023.
Ban hadu da G5 ba - Tinubu
Rahoto ya fito inda aka ji Bola Tinubu ya ce babu gaskiya a rade-radin da ke yawo cewa ya yi zama a boye da Gwamnonin PDP a kan batun takararsa a APC.
‘Dan takaran ya ce ya je Landan ne a kan hanyarsa ta zuwa Saudi Arabiya domin ya huta, kuma ya samu damar yin aikin Umrah ba don ya hadu da 'Yan G5 ba.
Asali: Legit.ng