Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada A Ji Ya Jinjinawa Obasanjo Kan Goyon Bayan Peter Obi a 2023
- Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya goyi bayan marawa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na LP baya da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi
- Obasanjo ya goyi bayan Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, ya kara da cewa tsohon gwamnan na jihar Anambra ya fi sauran yan takarar
- Ortom a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce idan da shi ba dan jam'iyyar PDP bane, da shine zai jagoranci yakin neman zaben Obi da kansa zuwa dukkan sassan Najeriya
Jihar Benue - Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue, ya goyi bayan mara wa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour baya da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi.
Obasanjo, cikin sakonsa na sabon shekara ga yan Najeriya, ya mara wa takarar shugabancin kasa Obi baya, yana mai cewa dan takarar na LP ya fi sauran yan takara, rahoton The Cable.
Wane dan takarar shugaban kasa Ortom ya ke goyon baya?
Da ya ke tsokaci kan batun a ranar Talata, Ortom ya ce idan da ace shi ba dan jam'iyyar PDP bane, da ya jagoranci kamfen Obi zuwa dukkan sassan kasar, rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ortom ya ce ya gamsu cewa Obi yana da halaye da ake bukata ga shugaban kasa na gaskiya wanda zai yi adalci, gaskiya da daidaito a mulkinsa ga kowa.
Gwamnan na Benue ya ce Obi zai kawo irin jagorancin da yan Najeriya ke bukata.
Wani sashi cikin sanarwar da kakakinsa Terver Akasa ya fitar, ya ce:
"Gwamna Ortom ya bawa yan Najeriya shawarar su zabi Peter Obi a matsayin mutumin da zai iya magance tattalin arziki, tsaro da sauran kallubale da kasar ke fuskanta."
"Gwamna Ortom ya sake jinjina wa Cif Olusegun Obasanjo saboda fadin gaskiya da kishin kasa a matsayinsa na dattijon kasa wanda ya kamata a mutuntuna ra'ayoyinsa kan harkokin da suka shafi kasa."
Goyon bayan da Obasanjo ya yi wa Peter Obi ta janyo cece-kuce galibi daga manyan jam'iyyun kasar biyu, inda APC ke cewa hakan baya nufin ra'ayin yan Najeriya kenan.
Ortom ya magantu kan yarjejeniyar da aka ce gwamnonin G-5 sun yi da Tinubu
A bangare guda, gwamnan na jihar Benue, Samuel Ortom ya ce gwamnonin na G5 ba su yi wata yarjejeniya da Bola Tinubu na APC ba game da zaben 2023.
Hakan ya saba da wasu rahotanni da suka fito a ranar Alhamis da ke cewa gwamnonin na G5 sun yi yarjejeniyar goyon bayan dan takarar na APC.
Asali: Legit.ng