Yadda Kyautar Kwankwaso Ta Taimaka Na Tsira Daga Harin Bam a Kaduna, Buhari

Yadda Kyautar Kwankwaso Ta Taimaka Na Tsira Daga Harin Bam a Kaduna, Buhari

  • Shugaban kasa Buhari ya sake jinjina kyautar mota SUV da Kwankwaso ya ba shi a kakar babban zaben 2015
  • A wani shiri da aka tsara, Buhari yace motar sulken da tsohon gwamnan Kano ya ba shi kyauta ta taimaka masa a harim bam din Kawo
  • A shekarar 2014 da ake shirye-shiryen zabe, an kaiwa Buhari harin bam a kasuwar Kawo dake birnin Kaduna

Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sake tabo zancen farmakin da aka kai masa a jihar Kaduna, shekara daya kafin babban zaben da ya lallasa Goodluck Jonathan.

Shugaba Buhari ya tsallake rijiya ba tare da samun rauni ba a tashin bam ɗin wanda ya auku a kasuwar Kawo dake birnin Kaduna, hadimansa uku suka jikkata aka hanzarta kai su Asibiti.

Rabiu Musa Kwankwaso da Shugaba Buhari.
Yadda Kyautar Kwankwaso Ta Taimaka Na Tsira Daga Harin Bam a Kaduna, Buhari Hoto: thecable
Asali: Twitter

A wancan lokacin, hadimin shugaba Buhari ya ce dan kunar bakin waken da ya kai harin wanda ya tuƙo Motar Toyota Sienna, ya kutsa cikin Ayarin Buhari sannan ya tashi bam din.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare, Tsohon Shugaban Kasa Ya Fadi Wanda Yake Goyon Baya Ya Gaji Buhari a Zaben 2023

The Cable tace Duk da shugaban ƙasan ya tsallake harin amma a Motar da yake ciki Toyota Land Cruiser da wata dake bayanta sun yi kaca-kaca sanadin harin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A shirin Fim ɗin da aka tsara mai taken, "Abubuwa masu mahimmanci game da Muhammdu Buhari," shugaban ƙasan ya ce motar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ba shi ta taimaka masa ya tsira daga harin.

Daily Trust ta rahoto Buhari na cewa:

"Kwankwaso mutum ne mai karamci da hangen nesa, shi ya bani kyautar motar sulke Land Rover. Ya gaya mun na yi amfani da ita domin tseren da na shiga ya kunshi masu son ganin baya na."
"Na fito zan tafi Kano daga Kaduna a cikin wannan motar kwatsam wata mota ta kutso zata wuce amma Dogarai na suka dakatar da su, ba zato suka tashi Bam."

Kara karanta wannan

Tsagin Atiku Abubakar Ya Fadi Gaskiya Game da Babban Asirin da Wike Ya Bankado Kan Zaben 2003

"Da na duba na ga sassan jikin mutane, mu dake cikin motar ko kwarzane bamu yi ba amma na ga jini a jikina saboda mutane da yawa bam din ya halaka."

- Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Malamai Sun Zane Ni Sosai Saboda Ina Gudun Zuwa Gonar Makaranta, In ji Buhari

A wani labarin kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya yi waiwayi kan irin rayuwar da ya yi a makaranta a lokacin da yake matashin saurayi.

Buhari, yace a wancan lokacin malamai na sadaukar da komai han harkar koyarwa, su yaba w amasu kwazo kana su hukunci dalibai marasa ji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel