Kar Ku Bar Najeriya a Hannun ‘Yan Ta’adda, Ortom ga Hukumomin Tsaro

Kar Ku Bar Najeriya a Hannun ‘Yan Ta’adda, Ortom ga Hukumomin Tsaro

  • Samuel Ortom, gwamnan jihar Biniwai ya bukaci hukumomin tsaro da su kara zage damtsa wajen shawo kan matsalar tsaro a 2023
  • Gwamnan ya kara da bukatar 'yan Najeriya da su bada gudunmawarsu ta hanyar bada bayanan da suka dace ga hukumomin tsaro don dakile ta'addanci a kasar
  • A cewarsa, jami'an tsaro su kadai ba za su iya magance matsalolin tsaro ba sai tare da agajin al'umma tare da yi wa 'yan Najeriya fatan alheri da tabbataccen farinciki

Binuwai - Samuel Ortom, gwamnan jihar Biniwai ya bukaci jami'an tsaro da su kara kokari a kan na da don shawo kan matsalar rashin tsaro a 2023, jaridar TheCable.ng ta rahoto.

Gwamna Samuel Ortom
Kar Ku Bar Najeriya a Hannun ‘Yan Ta’adda, Ortom ga Hukumomin Tsaro. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A wata takarda da Nathaniel Ikyur, sakataren watsa labaransa yasa hannu, Ortom ya kara kira ga 'yan Najeriya da su sa hannu don magance matsalar rashin tsaro.

Kara karanta wannan

2023: Idan Atiku Ya Hau Mulki Babu Dan Najeriyan Da Zai Kara Kwana da Yunwa, Gwamnan PDP

Ortom ya bayyana fatansa na ganin al'umma ta samu cigaba har 'dan kasa yana da damar aiwatar da kasuwancinsa yadda ya dace kamar yadda dokar shari'a ta bada dama a kowanne sashin kasar ba tare da tsoron cin zarafi ko tazarci ba.

A cewarsa, za a iya gina kasar ne

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

”idan muka bada gudunmawa a bangaren zabe don zabar shugabannin kwarai zuwa mukamai da dama a 2023."

Gwamnan jihar Biniwai ya ce yana da matukar mahimmanci 'yan kasa su guji bangarancin addini da al'ada.

Ya bukaci gwamnatin tarayya da tayi kokarin ganin ta shawo kan matsalar tsaro dake barazana ga zaman lafiyar Najeriya musamman ta sigar da zai bawa mutane natsuwa.

Ya koka game da halin tsaro a shekarar 2022 gami da rokon jami'an tsaro da su kara bada himma wajen magance mummunan lamarin.

Kara karanta wannan

Kwankwaso a Gusau Jihar Zamfara: Zan Ba Da Fifiko Kan Muhimman Abubuwa 2 Idan Na Ci Zaben 2023

"Ya isa haka. Ba zai yuwu ba a bar Najeriya a hannayen 'yan ta'adda a shekarar 2023 da kuma gans saboda karni mai zuwa a gaba.”

- A cewarsa.

Game da abun da gwamnatinsa tayi don tabbatar da tsaro a Biniwai, Ortom ya ce gwamnatinsa ta karfafa 'yan sa kai da jami'an tsaron dabbobi da karin motoci da babura don cigaban ayyukan tsaron hukumomin tsaro don dakile ayyukan ta'addanci da munanan ayyuka a jihar.

Ya bukaci mutanen jihar su kasance masu hada kai da hukumomin tsaron a koda yaushe ta hanyar samar da bayanai da duk wata gudunmawar da ta dace wanda zai taimaka musu a ayyukansu, inda yake cewa,

"Hukumomin tsaro ba za su iya su kadai ba sai da bada gudunmawar al'umma mara yankewa."

Daga bisani Ortom yayi fatan tabbatar zaman lafiya ga 'yan Najeriya da sabuwar shekara cike da farin ciki

”inda yayi fatan tabbataccen farin ciki ga mutane duk da halin matsalar tsaro da kalubalen tattalin arzikin da kasa ke fuskanta."

Kara karanta wannan

Wani Gwamnan Ya Sake Rokon 'Yan Bindiga Su Aje Makamai Gwamnatinsa Zata Yafe Masu

Abokin ya halaka abokinsa ‘Dan sanda

A wani labari na daban, wani ‘Dan sanda mai mukamin kofur ya sheka lahira bayan abokinsa yayi amfani da bindigarsa ya kashe shi.

Lamarin ya faru ne a farfajiyar wani bankin ‘yan kasuwa dake jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel