Yan Bindiga Sun Yi Wa Shugaban PDP Yankan Rago a Jihar Sakkwato

Yan Bindiga Sun Yi Wa Shugaban PDP Yankan Rago a Jihar Sakkwato

  • Miyagun yan bindiga sun yi wa shugaban PDP na gundumar Asare jihar Sakkwato yankan rago bayan dawowa daga Kamfe
  • Kauyen Asare na cikin karamar hukumar Gwadabawa, yankin da ta'addancin yan bindigan jeji ya yi wa katutu
  • Baya ga kisan shugaban PDP, maharan sun kuma harbe yayansa har lahira nan take

Sokoto - Rahotannin da muke samu yanzu haka sun nuna cewa a jiya Asabar wasu miyagun 'yan bindiga sun kai kazamin hari kauyen Asare dake ƙaramar hukumar Gwadabawa, jihar Sakkwato.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa yayin harin 'yan ta'addan sun yanka shugaban PDP na gundumar Asare kama suka bindige yayansa har lahira awanni bayan sun dawo daga Kamfen dan takarar gwamna.

Yan bindiga.
Yan Bundiga Sun Yi Wa Shugaban PDP Yankan Rago a Jihar Sakkwato Hoto: vanguardngr
Asali: Twitter

Mamacin mai suna Alhaji Iliyasu Agajiba, babban jigo ne kuma ginshikin PDP a yankin karamar hukumar Gwadabawa, wanda ya ba da dumbin gudunmuwa wajen ci gaban jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Martani Mai Zafi Ga Obasanjo Kan Nuna Goyon Baya Ga Peter Obi

Wasu na ganin wannan kisan gillan da aka yi wa shugaban PDP na gundumar ba zai rasa alaka da siyasa ba saboda lamarin ya faru ne awanni kadan bayan kaddamar da kamfen dan takarar gwamna a yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani abu da ya jan hankalin mutanen da suka rika tururuwar zuwa jaje da gane wa idonsu shi ne yanayi da kuma hanyar da maharan suka bi wurin raba Mamacin da rayuwarsa.

Makasan da ba'a san ko su waye ba sun yi amfani da wuka suka yanka marigayi shugaban PDP kana suka sa bindiga suka harbe yayansa har lahira wanda ya yi yunkurin taimaka masa.

Ƙaramar hukumar Gwadabawa a Sakkwato na ɗaya daga yankunan da 'yan fashin jeji ke cin karensu babu babbaka kuma ba tare da an taka masu birki ba.

Yadda harin ya faru

Kara karanta wannan

Kwamfuta Uwar Lissafi: 'Yar Jihar Kaduna Ta Amsa Tambayoyin Lissafi 34 Cikin Kasa Da Mintuna 3

A wani sunfurin labarin yadda harin ya auku, an ce makasan sun shiga garin a Babura 16, suka fara shiga gida-gida suna laluben dabbobin kiyo da duk abinda suka samu.

Yayin haka ne suka isa gidan shugaban PDP na gundumar da yayansa, inda suka yi ajalinsu baki ɗaya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Duk wani yunkuri na tabbatar da labarin daga bakin kakakin yan sandan Sakkwato, DSP Sanusi Abubakar, ya ci tura domin ba ya ɗaga kiran salula kuma bai ba da amsar sakonnin da aka tura masa ba.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kashe Basarake, Sun Yi awon Gaba da Wasu Uku a Jihar Neja

Alhaji Usman Garba, dagacin garin Mulo, ya rasa rayuwarsa ne a hannun yan ta'addan, waɗanda suka jefar da gawarsa suka tafi mutane uku.

A wata sanarwa da gwamnatin Neja ta fitar, gwamna Abubakar Sani Bello ya yi ta'aziyya tare da umartar dakarun tsaro su kamo maharan da suka aikata wannan ɗanyen aiki.

Kara karanta wannan

Tsagin Atiku Abubakar Ya Fadi Gaskiya Game da Babban Asirin da Wike Ya Bankado Kan Zaben 2003

Asali: Legit.ng

Online view pixel