Baraka ta Kunno G5, Wike Ya Fusata da Gwamnonin PDP kan Wanda Za a Marawa Baya

Baraka ta Kunno G5, Wike Ya Fusata da Gwamnonin PDP kan Wanda Za a Marawa Baya

  • Gwamnoni 5 da ake kai ruwa-rana da su a Jam’iyyar PDP ba su iya cin ma matsaya tsakaninsu ba
  • ‘Yan G5 sun rabu a kan ‘Dan takaran da za su ba goyon bayansu a zaben shugaban kasa mai zuwa
  • Wata shawara da aka bijiro da ita, ta harzuka Gwamna Nyesom Wike, ana zargin ya fice daga taron

London - Duk da rahotanni na ta yawo cewa ‘Yan kungiyar G5 sun amince su goyi bayan Bola Tinubu a 2023, an fahimci ba a tsaida magana ba.

Arise TV ta fitar da rahoto a ranar Juma’a, 30 ga watan Disamba 2022 cewa gwamnonin ba su ajiye magana kan wa za su ba goyon baya ba.

Ana tunanin Gwamna Nyesom Wike ya fice daga taron Landan ne cikin fushi, ya bar sauran abokan aikinsa, ya kama hanya zuwa birnin Madrid.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP Masu Rigima da Atiku Sun Fadawa Tinubu Abu 1 da Suke Bukata a Wajensa

Wata majiya ta shaida cewa a zaman da aka yi a kasar Birtaniya, kan gwamnonin bai hadu a kan wanda za su marawa baya a zaben shugaban kasa.

Bola Tinubu ko Peter Obi?

Rahoton ya ce Gwamna Seyi Makinde da Nyesom Wike su na ganin zai fi kyau su goyi bayan takarar Bola Tinubu da ya tsayawa a jam’iyyar APC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wani bangaren, akwai Gwamnonin Abia da Benuwai da suke da wani ‘dan takara a rai. Legit.ng Hausa ta na tunanin su na goyon bayan Peter Obi ne.

Wata majiya mai karfi ta shaidawa jaridar cewa a baya an ajiye magana cewa Bola Tinubu da Gwamna Makinde za su taimakawa junansu a zaben badi.

Gwamnonin PDP
'Yan G5 a Benuwai Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Ortom da Ikpeazu sun bada shawara G5 ta cire hannunta, ta guji fitowa karara ta goyi bayan wani ‘dan takara, domin hakan zai kawo masu matsala a PDP.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Bayan Ganawa Da Tinubu, Sanatan Arewa Ya Aika Da Sako Mai Muhimmanci Ga Wike Ga Gwamonin G5

Gwamnan Benuwai ya kawo shawarar a shiga yarjejeniya da shugaban PDP, Iyorchia Ayu. Wannan ya batawa Wike rai, ya fice daga wajen taron zuwa Sifen.

G5 sun hango matsala

Akwai yiwuwar cewa wasu daga cikin Gwamnonin da ke inuwar G5 sun tsorata da barazanar da PDP take yi na korarsu da kuma hana su yin takara a 2023.

Daga cikin ‘Yan G5 akwai wadanda suke takara a zabe mai zuwa, kuma kin goyon bayan Atiku Abubakar zai iya tsokano masu fushin jam’iyyar adawar.

Idan an kori wadannan Gwamnoni daga jam’iyya, PDP za ta fadawa INEC cewa sun rasa takararsu. Za a samu wannan rahoto a shafin Nairaland na yau.

Za a iya ladabtar da 'Yan G5

An samu labari cewa jam’iyyar PDP na kokarin koyawa Gwamnoninta Nyesom Wike, Okezie Ikpeazu, Samuel Ortom, Seyi Makinde da Ifeanyi Ugwuanyi darasi.

A tsari da dokar PDP, jam’iyya tana da wuka da nama da za ta iya ladabtar da duk wanda yake yin abin da zai jawo bakin jini ko kawo matsala a filin zabe.

Kara karanta wannan

Ganawar sirri: Daga karshe bayani ya fito bayan ganawar Tinubu da gwamnonin PDP 5 a Landan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng