APC Ba Zata Samu Kaso 25 Na Kuri'un Jihata Ba Zan Iya Shiga Caca, Gwamnan Edo

APC Ba Zata Samu Kaso 25 Na Kuri'un Jihata Ba Zan Iya Shiga Caca, Gwamnan Edo

  • Gwamna Obaseki na jam'iyyar PDP yace APC ba zata smau kashi 25 cikin 100 na kuri'un 'yan Najeriya mazauna jihar Edo ba
  • Gwamnan ya ce dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP zai samu nasara da gagarumin rinjaye a zabe mai zuwa
  • Obaseki yace 'yan Najeriya sun farga jam'iyyar APC ba zata iya komai ba, don haka suna bukatar sauyi

Edo - Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo yace jam'iyyar APC ba zata samu kaso 25% na kuri'un jiharsa ba a babban zaben 2023.

Da yake jawabi a wata hira da jaridar This Day ranar Laraba, Gwamna Obaseki yace Atiku Abubakar, mai neman zama shugaban kasa a inuwar PDP ne zai samu nasara mai girma a Edo.

Gwamnan Edo, Godwin Obaseki.
APC Ba Zata Samu Kaso 25 Na Kuri'un Jihata Ba Zan Iya Shiga Caca, Gwamnan Edo Hoto: thecable
Asali: UGC

Yace jam'iyyar APC mai mulkin ƙasa ta gaza kawo sauyin da 'yan Najeriya suka yi tsammani, inda ya bayyana cewa PDP ce kaɗai jam'iya mai rai a faɗin kasar nan.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Yi Magana a Kan Wa Za a Dauka Tsakanin Tinubu da Atiku a Katsina

"Ina hango ɗan takarar shugaban kasa na ya samu nasara da gagarumin rinjaye. Dokokin zabe sun sauya, a yanzun ba'a zancen karfin ikon jami'an tsaro ko INEC ta yi magudin zaɓe."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Mu ke da nasara a zancen gaskiya, karku manta na zauna a jam'iyun biyu, abinda kowa ya sani ne mafi yawan 'yan Najeriya sun amince APC ta gaza, ba zasu iya kawo sauyin da ake zato ba."
"Saboda haka 'yan Najeriya ba zasu cigaba da tafiya da su be, ya zama tilas mu canza canji. Bisa haka wane zaɓi gare mu? PDP domin ita ce kaɗai jam'iyya mai rai da ta yi saura a Najeriya."

- Godwin Obaseki.

Zan iya zuba kuɗina a caca kan kuri'un Edo - Obaseki

Gwamnan ya kara da cewa tsawon shekaru 12 jam'iyyar PDP na tsagin Adawa a jihar Edo amma tana dawo wa kan mulki na shekaru biyu kacal ta rusa jam'iyar APC.

Kara karanta wannan

Babban Jigon Siyasa Ya Bayyana Abinda Ka Iya Faruwa da APC, Tinubu a Zaben 2023

A ruwayar The Cable, Obaseki yace:

"APC ba zata samu kaso 25 cikin 100 na kuri'un jihar Edo ba. Dagaske nake kan wannan zancen kuma a shirye nake na shiga caca da kuɗina kan haka."

Obaseki ya ƙara da cewa Atiku Abubakar da shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, sun fahimci abinda ke wakana a jam'iyya kuma zasu farfaɗo da ita.

G5 zasu gana da Tinubu a Turai

A wani labarin kuma Wike da Gwamnonin PDP Hudu Zasu Gana da Bola Tinubu Game da 2023

Ga dukkan alamu gwamna Wike da sauran yan tawagarsa ta G-5 sun ɗauki matsaya kan wanda zasu marawa baya a zaben shugaban kasa 2023.

Gwamnonin guda 5 da suka raba gari da Atiku, zasu sa labule da ɗan takarar APC, Bola Tinubu a nahiyar Turai a wannan makon don karkare zance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel