Gwamnan PDP Ya Bada Dalilin Garkame Ofishin Yakin Neman Zaben Atiku a Jiharsa

Gwamnan PDP Ya Bada Dalilin Garkame Ofishin Yakin Neman Zaben Atiku a Jiharsa

  • Gwamnatin Nyesom Wike ta bada umarni a rufe wani ofishi da jam’iyyar PDP take kamfe a Ribas
  • A yanzu an garkame ofishin yakin neman zaben Atiku Abubakar/Ifeanyi Okowa a GRA a Fatakwal
  • Ana zargin Jam’iyyar PDP da bude ofishin kamfe a wurin da za a rika addabar mazaunan da hayaniya

Rivers - Ana zargin Gwamna Nyesom Wike ya bada umarni an rufe wani ofishin yakin neman zaben Atiku Abubakar/Ifeanyi Okowa a jihar Ribas.

People Gazette ta ce wannan ofishin kamfe da ake rufe yana unguwar GRA ne a garin Fatakwal. Hakan ya nuna har gobe akwai baraka a jam’iyyar PDP.

Dalilin da gwamnatin Ribas ta bada wajen rufe ofishin shi ne ana amfani da shi wajen damun mazauna yankin da hayaniya ba da izinin hukuma ba.

Gwamnatin Nyesom Wike tayi amfani da dokokin gwamnatin jiha masu cikakken iko na 21 & 22 wajen daukar wannan mataki da ake ganin siyasa ce.

Kara karanta wannan

Dubbannin Malaman Makaranta a Arewa Sun Yunkuro, Sun Ayyana Wanda Zasu Goyi Baya a 2023

A rahoton da Sahara Repoters ta wallafa a yammacin Juma’a, an ji cewa ana zargin an bude wadannan ofisoshin ne a filin da ake gina wuraren zama.

PDP PCC ta nemi izinin Ribas

Kafin a kai ga haka, kwamitin yakin neman zaben PDP ya rubuta takarda zuwa ga gwamnatin Ribas domin neman izini kafin ayi amfani da ofishin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yakin Neman Zaben Atiku Abubakar a Jihar Katsina
Atiku Abubakar yana kamfe Hoto: @Atiku
Asali: Facebook

Tun lokacin da kwamitin neman takaran jam’iyyar ya rubuta wasikar neman izinin, gwamnati ba ta ce komai ba, sai a yau kurum aka ga an rufe ofishin.

Kwamitin kamfe ya yi tir

Kwamitin kamfen jam’iyyar PDP na reshen jihar Ribas, ya yi Allah-wadai da wannan mataki da aka dauka, ya ce an yi wa damukaradiyya hawan kawara.

Kamar yadda kwamitin ya sanar a wani jawabi, gwamnatin Ribas ta rufe ofishin ne duk da bai dauke da hotuna ko fostar wani ‘dan takaran PDP a 2023.

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala Ta Kunno a PDP Yayin da Atiku Abubakar Da Tawagarsa Zasu Shiga Katsina Yau

Kwamitin ya ce da gangan aka ki amincewa da bukatarsu na amfani da ofishin domin ayi masu wulakancin da suka ce ya sabawa doka da tsarin kasa.

Za a je kotu - PCC

Matakin da masu taya jam’iyyar yakin neman zaben 2023 a Ribas za su dauka shi ne su kai kara zuwa kotu domin an keta masu alfarmar da doka ta ba su.

PDP PCC ya nuna yadda mulkin Hitler ya shude a kasar Jamus, haka za ayi lokacin da za a karbe mulki daga hannun Gwamnati Nyesom Wike mai-ci a Ribas.

NNPP tayi kamu a Gombe

An ji labari cewa tsohon Daraktan kamfen Gwamna na Muhammad Inuwa Yahaya a zabukan Jihar Gombe ya fice daga jam’iyyar APC ya koma NNPP.

Musa Zubairu ya ce ya koma jam’iyyar NNPP mai kayan dadi ne domin ya taimaka Khamisu Ahmed Mailantarki a zaben Gwamna da za ayi a 2023.

Kara karanta wannan

2023: An Yi Zaman Sulhu da Gwamna Wike Na Karshe, Sakamakon Ya Ja Atiku Ya Ɗauki Babban Mataki

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng