Katsina: Malaman Makarantu Sun Ayyana Goyon Baya Ga Dikko Radda a 2023

Katsina: Malaman Makarantu Sun Ayyana Goyon Baya Ga Dikko Radda a 2023

  • Malaman Makarantu a jihar Katsina sun ce ba za'a barsu a baya ba, sun ayyana goyon bayansu ga ɗan takarar APC
  • Dakta Dikko Radda, mai neman zama gwamnan Katsina a 2023 ya taba aikin koyarwa a tarihin rayuwarsa
  • A cewar Malaman suna hangen gyaruwar bangaren ilimin jihar idan ya kai ga matsayin gwamna

Katsina -Aƙalla Malaman makaranta 5,000 da suka kunshi malaman makarantun gwamnati da na al'umma a Katsina ne suka ayyana goyon bayansu ga Dikko Radda, ɗan takarar gwamna a inuwar APC.

Dubbannin Malaman sun bayyana matsayarsu ne a wani Rali da kwamishinan ilimi na jihar, Farfesa Badamasi Lawal Charanchi, ya jagoranta a Filin Karkanda ranar Litinin.

Taron Malaman Malaman Makarantu a Katsina.
Katsina: Malaman Makarantu Sun Ayyana Goyon Baya Ga Dikko Radda a 2023 Hoto: channelstv
Asali: UGC

Channels tv tace an ga Malaman cike da farin da annashuwa a fuskoninsu domin a wurinsu, mai ceto ya zo, wanda suke sa ran zai farfaɗo da bangaren ilimi a Katsina.

Kara karanta wannan

Rikicin APC Ya Dauki Sabon Salo, Majalisa Ta Tsige Ciyaman Daga Mukaminsa a Jihar Arewa

A cewar kwamishinan ilimin, waɗanda suka halarci ralin sun haɗa da shugabannin Firamare 2,800, shugabannin Sakandiren gwamnati 600 da na Sakandiren al'umma 160 da wasu malamai masu gudanarwa sama da 500.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace an zakulo Malaman da suka halarci wurin daga ma'aikatar ilimi ta jiha, hukumar kula da ilimin bai ɗaya SUBEB da jami'an kula da ilimi na shiyya-shiyya.

Kwamishinan ya bayyana cewa ba ya ga kasancewar Dikko Radda tsohon malamin makaranta, jagora ne mai saurin daukar abu wanda zai yi duk me yuwuwa wajen habaka ilimi.

Farfesa Lawal Charanchi yace:

"Mun ga abinda Masari ya yi a shekaru Bakwai da suka gabata a ɓangaren Ilimi wanda ya ba fifiko. Ya zuba dukiya musamman wajen samar da kayan aiki, walwalar ɗalibai, gina azuzuwa da ɗaukar sabbin malamai."
"Mu a matsayin malamai muna da damar nazari mu gani wane ɗan takara zai ɗora, mun gano wanda ya dace a APC, wanda shi kansa Malami ne kuma yana ji a ransa mu ke da nauyin tabbatar da ilimi mai inganci."

Kara karanta wannan

Rigimar PDP: "Saura Kiris" Gwamnan Tsagin Wike Ya Faɗi Yuwuwar Su Yi Wa Atiku Aiki a 2023

"Bamu shiga lamurran siyasa amma kowa na da hakkin ya kulla alaƙa da duk wanda yake so, kwansutushin ya bamu dama. Bana ganin rashin kyautawa don mun goyi bayan wani ɗan takara."

Wasu malamai biyu, yayin da suke kore jita-jitar da ake yaɗawa a wurin Ralin sun ce ba wanda ya tilasta masu zuwa gangamin, a karan kansu ne suka ga ya dace su goyi bayan ɗan takarar APC.

Legit.ng Hausa ta zanta da wani Malamin Makaranta wanda aka ɗauka a tsarin S-Power, Saifullahi Lawal, yace fatansa idan Raɗɗa ya kai ga nasara ya cika alkawarin da Masari ya ɗaukar masu.

Malami mai aiki a makarantar Sakandiren gwamnati dake Dabai, ƙaramar hukumar Danja, yace duk da ba kowa aka gayyata taron ba amma yana tare da wannan matakin na 'yan uwansa.

Saifullahi yace:

"Ni dama can shi ne zaɓina don haka ina tare da Malaman 100 bisa 100. Amma ina rokon ɗan takarar APC idan Allah ya ba shi mulki ya dube mu ('yan Spower) ya maida mu cikakkun ma'aikata."

Kara karanta wannan

2023: An Yi Zaman Sulhu da Gwamna Wike Na Karshe, Sakamakon Ya Ja Atiku Ya Ɗauki Babban Mataki

Wani malamin makarantar al'umma na daban, Umar Idris, ya nuna shakkunsa kan wannan mataki inda ya shaida wa wakilinmu cewa kundin doka be ba malami dama ya yi haka ba.

A cewar Umar, shugaban Ideal Academy Kahutu, "Inda ace wani ɗan takara daban suka goya wa baya wane mataki kake tsammanin gwamnati zata ɗauka. Zan zaɓi Dikko amma abinda suka yi ya saba wa dokar koyarwa."

APC ta kara karfi a jihar Katsina

A wani labarin kuma Ɗan takarar APC a Katsina ya samu gagarumin goyon baya yayin da jam'iyya guda ta rushe zuwa cikin jam'iyya mai mulki

Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyar PRP ta yanke shawarin mara wa Dikko Raɗɗa baya a 2023 saboda manufofinsu sun zo ɗaya.

Mamba a kwamitin yakin neman zaɓen Dikko/Jobe 2023 ya tabbatar mana da haka a wata hira ta wayar tarho, yace sun kunshi shugabannin PRP da yan takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel