Zabe ya karaso, Hukumar INEC ta Jero Manyan Abubuwa 2 da take Tsoro a 2023
- Hukumar INEC ta damu da yadda ake kai mata hare-hare a lokacin da ake shirye-shiryen zabuka
- Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu yace akwai matsala idan harin suka kai badi
- Yakubu ya ce bayan matsalar rashin tsaro, abin da suke tsoro shi ne sayen kuri’u da ‘yan siyasa ke yi
FCT, Abuja - Hukumar gudanar da zabe na kasa watau INEC ta damu da yadda ake kai mata hare-hare a lokacin da take kokarin shirya zaben 2023.
Punch ta rahoto INEC ta na cewa wadannan miyagun hare-hare da ake kai mata, sun zama barazana ga zaben da ake shirin gudanarwa a shekarar badi.
Haka zalika hukumar ta koka da cewa kokarin da tayi a baya wajen yakar sayen kuri’u da ake yi a Najeriya, bai yi aiki ba, take cewa hakan cikas ne.
Hukumar mai cin gashin kanta, tayi wannan bayani ne a wajen wasu taro da aka yi jiya a Abuja.
An yi taron karawa juna sani
Shugaban INEC na kasa, Mahmood Yakubu ya yi jawabi a wajen taron karawa juna sani da makarantar sojojin Najeriya ta shirya a ranar Litinin dinnan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Mahmood Yakubu ya yi magana a kan abin da ya shafi rigimar zabe da tsaro, ya ce idan ana son ayi zabe na kwarai, dole a daina kai masu hari.
An rahoto Farfesan yana cewa idan wadannan munanan hare-hare suka cigaba har zuwa shekara mai zuwa, za su yi tasiri wajen shirya zabe na kwarai.
Idan aka yi sake, babu wanda zai ci zabe
Shugaban na INEC ya kuma nuna muddin ba a samu zaman lafiya a wasu bangarorin kasar nan ba, hakan zai kawowa ‘yan takara cikas wajen lashe zabe.
A doka, wajibi ne sai ‘dan takara ya samu akalla 25% na kuri’un da aka kada a mafi yawancin jihohin kasar nan sannan za a iya zama shugaban Najeriya.
Kwamishinan yada labarai da wayar da kan al’umma, Festus Okoye ya wakilci shugaban INEC a wajen taron, ya yi bayanin kokarin da hukumar ke yi.
An kai wa INEC hari sau 50 - Yakubu
Okoye ya ce daga zaben 2019 zuwa yanzu, an kai wa INEC hari sau 50 a jihohi 15. Jami’in yake cewa hare-haren da ake kai wa shekarar nan sun fi hadari.
Hukumar ta ce ta fara maye gurbin na’urorin BVAS da ta rasa a sakamakon hare-haren, ta ce za a tanadi wasu kayan aikin zaben kafin karshen shekara.
A wajen wani taro da MacArthur Foundation ta shirya a garin Abuja, shugaban na INEC ta yi magana ne a kan hadarin kudi wajen murde zabe a Najeriya.
Yakubu ya tabbatarwa jama’a ba za ta yiwu a iya yin magudi da na’urorin BVAS ba, ya ce hanyar da ta rage ita ce sayen PVC ko amfani da kudi a samu kuri’a.
An daure DG a LP
A karshen shari’arsa da Hukumar EFCC, an ji labari Kotu ta samu Dr. Doyin Okupe da laifin karbar kudin makamai a lokacin mulkin Dr. Goodluck Jonathan.
Alkali ya yankewa Dr. Okupe daurin shekaru biyu a kurkuku, amma ba zai yi zaman gidan yarin ba domin 'dan siyasar ya biya tarar N13m da aka ci shi.
Asali: Legit.ng