Kudin Makamai: Tsohon Hadimin Jonathan Ya Biya N13m, Ya Gujewa Shiga Kurkuku

Kudin Makamai: Tsohon Hadimin Jonathan Ya Biya N13m, Ya Gujewa Shiga Kurkuku

  • Doyin Okupe ba zai tafi gidan yari ba duk da hukuncin da Alkalin kotun tarayya ya zartar masa
  • Darekta Janar na yakin neman zaben Peter Obi a LP ya biya tara a maimakon ya tafi kurkuku
  • Dr. Okupe ya biya N13m domin wanke kan sa daga laifuffuka 26 da EFCC ta same shi da aikatawa

Abuja - Darekta Janar na kwamitin yakin neman zaben Peter Obi, Dr. Doyin Okupe ya biya N13m a matsayin tarar sabawa dokar hana safarar kudi.

The Cable a rahoton da ta fitar a ranar Litinin, 19 ga watan Disamba 2022, ta ce kotu ta kama Doyin Okupe da wasu laifuffukan da EFCC take zarginsa.

A dalilin haka Alkali Ijeoma Ojukwu na babban kotun tarayya a Abuja ya daure ‘dan siyasar na shekaru biyu ko kuma ya biya tarar kudi, N13m.

Kara karanta wannan

Daraktan Yakin Neman Zaben Peter Obi Zaiyi Zabe A Kurkuki, Sakamakon Umarnin Kotu Na A Tsareshi

‘Dan siyasar ya zabi ya biya tara a kan duka laifuffuka 26 da aka same shi da aikatawa, hakan ta sa ya biya N13m kafin 4:30 na yammacin jiya.

Hukumar dillacin labarai na kasa ta ce sharadin da aka bada shi ne dole a biya tarar kafin lokacin. Binciken da aka yi ya nuna Okupe ya biya tarar.

Badakalar Kudin makamai

Okupe wanda yayi aiki a matsayin Mai taimakawa Goodluck Jonathan wajen hulda da jama’a, ya karbi kudi a hannun Sambo Dasuki ba tare da bin doka ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Doyin Okupe
DG LP PCC, Doyin Okupe Hoto: www.arise.tv
Asali: UGC

Dasuki ya rike ofishin NSA, Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro a lokacin da Goodluck Jonathan yake mulki kafin Mayun 2015.

A haka ne Mai shari’a Ijeoma Ojukwu na kotun da yake Abuja ya samu jagoran na jam’iyyar LP da sabawa sashe na 16(1)&(2) na dokar safarar kudi.

Kara karanta wannan

Yaro Dan Shekaru 10 Ya Aika Gagawrumin Sako Ga Peter Obi Kan Zaben 2023, Bidiyon Ya Yadu

Babu maganar gidan kaso

A maimakon ya tafi gidan yari na tsawon shekaru biyu, Punch ta ruwaito ‘dan siyasar ya zabi biyan tarar da kotu ta yanke masa domin ya huta da zaman kaso.

Idan da an daure Okupe, babu mamaki ba zai samu ‘yanci ba sai a shekarar 2024, alhali shi ne shugaban kwamitin yakin neman zaben Peter Obi a LP.

‘Dan takaran shugaban kasa a LP, Peter Obi da mabiyansa sun nuna wannan hukunci da aka yanke ba zai shafi neman takaran da suke yi a zabe mai zuwa ba.

Kwanan baya wasu magoya bayan LP suka huro wuta sai Okupe ya sauka daga mukamin da yake kai saboda zargin bai biyan kudin zama a jam’iyya.

An ba Isa Ali Ibrahim Pantami Dakta

An ji labari masana da manya sun jinjina yayin da Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya samu kyautar Digirin Dakta daga Jami’ar Achievers University.

Kara karanta wannan

Kudin makamai: Tashin hankali ga dan takarar shugaban kasa, kotu ta daure jigon kamfen dinsa

Shugaban NUC na kasa, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ya yabi Ministan bayan shugaban jami’ar, Yakubu Dogara ya ba shi kyautar Digirin digir-digir

Asali: Legit.ng

Online view pixel