Kotu Ta Daure Darakta Janar Na Yakin Neman Zaben Peter Obi Shekara Biyu A Gidan Yari

Kotu Ta Daure Darakta Janar Na Yakin Neman Zaben Peter Obi Shekara Biyu A Gidan Yari

  • Kotu ta kama darakta janar na yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Lp, da laifin satar dukiyar kasa
  • Wata kotu ta daure Doyin Okupe a gidan dan kande tsawon shekara biyu domin yaje ya gyara halinsa.
  • Tsohon mai taimakawa tsohon shugaban kasa Jonathan, Doyin, an zargeshi ne da wawure kudi har N720m

Abuja: An yankewa daraktan janar na yakin neman zaben dan takarar jam'iyyar LP, hukuncin dauri tsawon shekara biyu a gidan yari, bisa kamashi da laifin wawasuhe kudin gwamnati, ciki harda wasu N240m da ya kasa bayani.

Mai shari'a Ijeoma Ojukwu yace an samu wanda ake tuhuma da laifi 26 cikin laifuka 59 da ake zarginsa da su. dan haka kotu ta yanke masa hukuncin dauri. Rahotan jaridar The Nation

Mai shari'a yace Doyin na da laifi 59 da aka zargi shi da shi anan gaban kotu, wanda suka hada zamba cikin aminci, wawushe dukiyar al'umma, da kuma motsin wasu kudade da aka ga giftawarsu zuwa asusunsa daga tsohon ofishin mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro.

Kara karanta wannan

Kudin makamai: Tashin hankali ga dan takarar shugaban kasa, kotu ta daure jigon kamfen dinsa

Peter
Kotu Ta Daure Darakta Janar Na Yakin Neman Zaben Peter Obi Hoto: The Nation
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai Ya Aikata Ne!

To sai dai mai shari'a yace hukumar EFCC, ta kasa kawo kwararan dalilai a tuhume-tuhume 33 da take masa, dan haka ta yanke masa hukunci da sashe na 1(a) da (b) na dokar satar kudin gwamnati ta 2009 wanda hukuncinta yake kasan sashi 16(a) da 16(2)(b).

Kotun tace ta lura da yadda wanda ake zargin baiyi musun wasu kudaden da ake zargin Doyin da debesu ba. Alkalin Kotun yace ya lura da yadda shi Doyin din yake gudanar da wasu aiyuka wanda ba karkashin ofishinsa suke ba lokacin da yake hadimin Jonathan

To sai dai akasan hukuncin kotu ta sanyawa wanda ta kama da laifin tarar da zai biya, in baya son zuwa gidan kaso, kuma ya biya nan take.

Kara karanta wannan

Kotu ta Wanke Hadimin Gwamna Mai Gidaje 220 masu Kimar N1.8b, ICPC Zata Daukaka Kara

Jaridar Vanguard ta rawaito wanda ake tuhumar ya ringa karbar kudi muraran lokacin da yake ofishin hadimin shugaban kasa, sannan ya hana shigar da bayannan kudin da yake karba daga ofishinsa.

Laifin da ya aikata ya dace da hukuncin da zan zartar masa yanzu, inji mai shari'a Ojukwu yayin da take kokarin karanto hukuncin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel