‘Yan Takara Sun Kunyata Atiku, Sun Ki Yarda Suyi Masa Aiki a Kwamitin Takaran 2023

‘Yan Takara Sun Kunyata Atiku, Sun Ki Yarda Suyi Masa Aiki a Kwamitin Takaran 2023

  • Wasu da aka zaba su yi aiki a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a PDP sun ki karbar aikin
  • ‘Yan takaran majalisar tarayya a jihar Ekiti sun fadawa Aminu Tambuwal ba za suyi wa PDP aiki ba
  • Dalilinsu kuwa shi ne an dauko ‘yan jam’iyyar SDP a Ekiti, an cakuda a cikin kwamitin yakin zaben

Ekiti – Rikicin PDP ya cabe a jihar Ekiti domin masu neman takarar majalisar tarayya da ‘dan takaran Gwamna sun ki yadda suyi wa jam’iyya aiki.

Vanguard ta ce wasu ‘yan siyasa da-dama daga jihar Ekiti sun yi watsi da nada su da aka yi a cikin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP.

Darekta Janar na kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Aminu Waziri Tambuwal ya fitar da sunayen wadanda za su taya jam’iyyar kamfe.

Kara karanta wannan

Hamza Al-Mustapha da Wasu ‘Yan Takara da Ya Kamata a Lura da Su da Kyau a 2023

‘Yan takaran kujerar Sanatoci a PDP, Alhaji Lateef Ajijola da Funso Ayeni sun nesanta kan su daga jerin ‘yan kwamitin da Aminu Waziri Tambuwal ya fitar.

Na-kusa da Fayose sun ja baya

Rahoton ya ce Lere Olayinka, Hon. Mrs. Emiola Adenike Jennifer, Otunba Babatunde Ajayi da Joju Fayose duk ba su amince su taya Atiku kamfe a 2023 ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lere Olayinka shi ne Mai magana da yawun bakin Ayodele Fayose, shi kuma Joju Fayose yaron tsohon Gwamnan ne, duk su na takarar majalisar tarayya.

Atiku
PDP a wajen kamfe a Imo Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

"An dauko 'yan wata jam'iyya"

A wata wasika da ‘yan takaran suka aikawa Gwamna Tambuwal, sun ce mafi yawan wadanda aka zaba a kwamitin yakin neman zaben ba ‘yan PDP ba ne.

A cewarsu, ‘yan SDP aka dauka, aka sa a kwamitin da za su yi wa PDP aiki, sannan suka ce mafi yawan wadanda aka zaba a PDP, ba su da tasiri a jihar.

Kara karanta wannan

In dai Inyamurai Na Son Shugabancin Kasa Su Zabe Ni, Inji Atiku Abubakar

Korafin wadannan ‘yan siyasa shi ne an kinkimo mutanen da sun bar PDP zuwa SDP a lokacin zaben Gwamna da aka yi, kuma har yanzu ba su dawo ba.

A dalilin haka, wadannan ‘yan siyasa da aka zaba suka ce ba za su amince su yi wa PDP aiki ba, suka bukaci ayi amfani da sunayen farko da su ka bada.

Bisi Kolawole wanda ya nemi takarar Gwamna a zaben jihar Ekiti, ya ce har gobe yana nan a jam’iyyar PDP, amma ba zai karbi nauyin da aka ba shi ba.

Otunba Bisi Kolawole ya ce ba zai yarda ya yi aiki da wadanda suka yake shi a zaben Gwamna ba. Kolawole ya sha kashi a hannun Biodun Oyebanji

An kona ofishin PDP

Labari mara dadin da magoya bayan PDP da masu kaunarshi suka samu a makon jiya shi ne wasu kona ofishin kamfen jam’iyyar adawar a Gombe.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Irin Na Tinubu, Ya Tafka Katuwar Katobara Gaban Jama’a Wajen Kamfe

Mataimakin Darekta Janar na kwamitin yakin neman zaben Atiku/Dan Barde a 2023 yace ‘ya ‘yan jam’iyyar APC ne suka yi masu ta’adin nan ba kowa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng