Rikici Ya Kara Tsanani, Gwamna Wike Ya Sha Alwashin Ba Zai Bar Arewa Ta Mamaye Komai a PDP Ba

Rikici Ya Kara Tsanani, Gwamna Wike Ya Sha Alwashin Ba Zai Bar Arewa Ta Mamaye Komai a PDP Ba

  • Gwamna Nyesom Wike, ya lashi takobin cewa ba zai taba yarda ‘yan Arewa su ci gaba da mamaye manyan mukamai a jam'iyyar PDP ba
  • Gwamnan na jihar Ribas ya yi furucin ne yayin da ya karbi bakuncin yan takarar PDP daga jihar Cross River a Port Harcourt
  • Shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da DG na kwamitin kamfen, Aminu Tambuwal duk yan arewa ne

Rivers - Yayin da rikici ke kara kamari a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya sha alwashin cewa, ba zai bari 'yan Arewa su ci gaba da mamaye manyan kujeru a jam'iyyar ba.

Wike ya yi watsi da tsarin da jam’iyyar ke kai a yanzu haka inda manyan masu rike da mukamai suka fito daga yankin arewacin kasar.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Kinkimo Manya 3 Domin Su Lallabi Wike Ya Marawa PDP baya

Atiku da Wike
Rikici Ya Kara Tsanani, Gwamna Wike Ya Sha Alwashin Ba Zai Bar Arewa Ta Mamaye Komai a PDP Ba Hoto: Atiku Abubakar, Gov Nyesom Ezenwo Wike - CON
Asali: Facebook

Shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu; dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Aminu Tambuwal duk 'yan arewa ne.

Gwamnan na Ribas ya ce babu wanda zai iya shawo kansa domin ya ajiye wannan fafutuka nasa na tabbatar da damokradiyya a cikin jam’iyyar, Channels tv ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana hakan ne a daren ranar Laraba, 12 ga watan Oktoba, yayin da ya karbi bakuncin yan takarar PDP da shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi daga jihar Cross River a gidansa da ke Port Harcourt.

A wajen taron, ya bayar da gudunmawar motocin bas guda 25 don tallafawa kamfen dinsu.

Tawagar yan takarar na PDP daga jihar Cross River sun kaiwa Wike ziyarar ban girmane .

Sun jinjinawa Wike kan goyon bayan da yake basu tun bayan da gwamnansu, Ben Ayade ya sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ana tsaka da shirin 2023, wata jam'iyya ta kori dan takarar shugaban kasanta

Wike ya dauki alkawarin marawa PDP reshen Cross River baya, yayin da ya karfafawa yan takarar gwiwar ganin sun yi nasara a zaben.

Rikici Ya Kara Kamari Tsakanin Atiku da Wike, PDP Ta Dage Yakin Neman Zaben 2023

A gefe guda, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ɗage yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na wani ɗan lokaci saboda takun sakar da aka jima ana yi tsakanin Atiku Abubakar, Gwamna Nyesom Wike.

The Nation ta tattaro cewa an ɗage Kamfen ne bisa alfarmar Atiku, wanda majiya daga jam'iyyar tace ya haɗa fitattun jiga-jigan PDP da zasu shiga tsakaninsa da gwamnan jihar Ribas.

Bayanai sun nuna cewa Atiku ya zakulo tsohon shugaban majalisar Dattawa, David Mark, tsohon gwamnan jihar Ribas, Peter Odili, da tsohon gwamnan Delta, James Ibori, a matsayin masu sulhunta tsakani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel