Zan Karar Da ’Yan Bindiga Idan Kuka Zabe Ni Na Gaji Buhari, Tinubu Ga Al’ummar Kaduna
- Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC ya bayyana cewa, zai yi aiki tukuru wajen tabbatar da ya kawo karshen ‘yan bindiga a Kaduna
- Bola Tinubu ya ce El-Rufai ya yi kokari a shekarun da ya yi yana mulki a Kaduna, kuma hakan abin a yaba ne
- ‘Yan bindiga sun kashe mutane kusan 2,000 tare da sace akalla 6,000 cikin kasa da shekaru biyu a Kaduna
Jihar Kaduna - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya yi alkawarin kawo karshen rikicin ‘yan bindiga a Kaduna da yankin Arewa masu Yamma a Najeriya.
Ya bayyana hakan ne yayin da ya ziyarci jihar domin kaddamar gangamin kamfen dinsa a yankin na Arewa maso Yamma a jihar Kaduna, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.
Jihar Kaduna dai na daya daga cikin jihohi bakwai na Arewa maso Yamma da ke fama da tashe-tashen hankula daga ‘yan bindiga da barayin daji da ke aikata ta’addanci kan mazauna.
Da yake bayyana matsayarsa ga yaki da ta’addanci, Tinubu ya ba zai bar ‘yan ta’adda su ci karensu babu babbaka ba, domin kuwa zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Arewacin Najeriya da ma sauran yankunan kasar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda barnar ‘yan bindiga ta dai-daita jama’a a Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce, akalla mutane 1,192 ne ‘yan bindiga suka kashe, yayin da suka yi garkuwa da matafiya, dalibai da gama garin jama’a da suka kai akalla 3,000 a 2021.
Wani rahoton gwamntin ya ce, daga Janairu zuwa Satumban 2022, akalla mutane 800 aka kashe tare da sace mutum 1,200, inji kididdigar da gwamnatin ta yi, Channels Tv ta ruwaito.
A nasa bangaren, Tinubu, wanda tsohon gwamnan jihar Legas ne ya duba ilahirin jama’a ya shaida musu cewa, zai kawo karshen rikicin ‘yan bindiga, barnarsu za ta zama tarihi a jihar.
Ya kuma bayyana cewa, gwamna El-Rufai na Kaduna ya yi aiki tukuru kuma abin a yaba tun daga hawansa a 2015 zuwa yanzu.
Saboda haka ne ma ya bukaci ‘yan APC da sauran mazauna a jihar da su ba da kuri’unsu ga dan takarar da El-Rufai ya tsayar domin ya gaje shi a zaben 2023.
Wani rahoton ya ce, Tinubu ya kai ziyara Birnin Gwari domin jajantawa wadanda hadurran 'yan bindiga ya shafa a yankin.
Asali: Legit.ng