An Wulakanta Babban Jigo a APC, Tsageru Sun Yi Masa Tsirara a Bainar Jama’a
Ana zargin wasu bata-garin matasa sun tube Abubakar Abu Giza a wajen gangamin siyasa a Nasarawa
Abubakar Giza yana cikin jiga-jigan da jam’iyyar APC mai mulki take ji da su a jihar Arewa maso tsakiyar
Shugaban IPAC na reshen Jihar, Hon. Cletus Ogah ya fitar da jawabi, yana mai tir da abin da ya auku
Nasarawa - Shugaban IPAC mai kula da harkar jam’iyyu a jihar Nasarawa, Cletus Ogah Doma ya yi tir da abin da aka yi wa Abubakar Abu Giza.
A ranar Juma’a, 9 ga watan Disamba 2022, Vanguard ta rahoto Hon. Cletus Ogah yana mai tir da yadda wasu suka wulakanta jigon na jam’iyyar APC.
Cletus Ogah ya yi magana ne bayan an ga wani bidiyo da ake cin zarafin Abubakar Abu Giza, wasu matasa suka yi kokarin masa tsirara cikin taro.
Ana zargin wasu da ke goyon bayan jam’iyyar APC ne suka yi wannan rashin mutunci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hon. Cletus Ogah ya gargadi matasa
Yayin da aka buga gangar zaben 2023, an rahoto Ogah Doma yana gargadin matasan jihar Nasara a kan shiga bangar siyasa, yace yin hakan bai dace ba.
Doma yace bai kamata a rika amfani da manyan gobe wajen rigimar siyasa ba, yake cewa a duk lokacin da aka samu sabani, bai dace matasa su shiga ba.
Ogah Doma wanda shi ne shugaban jam’iyyar Zenith Party ya kira abin da aka yi wa jagoran na APC a matsayin dabbanci, yace dole ne ayi tir da danyen aikin.
Shugaban na IPAC ya bada shawara ga APC mai mulki da sauran jam’iyyun siyasa su fito duk suyi Allah-wadai da abin da ya faru, musamman ganin zabe ya zo.
‘Dan siyasar yake cewa bai kamata a bar mokamar zaben 2023 a hannun bata-garin ‘yan siyasa ba.
Ba Shugaban APC na kasa ba ne
Wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta gani a yau ya nuna yadda aka nemi a wulakanta Abu Giza kafin wasu su suturce shi da babbar riga a wajen wani taron siyasa.
Wasu suna jita-jitar shugaban APC na kasa ne aka yi wa wannan wulakanci.
A jawabin shugaban na IPAC na reshen jihar Nasarawa, ya yi kira ga daukacin al’umma su hujewa tada zaune tsaye da jawo rikici yayin da ake yakin takara.
Gwamnan Legas ne Uba na
An ji labari wani ‘Dan shekara 27 mai suna Emmanuel Sanwo-Olu yace mahaifiyarsa ta fada masa cewa ba kowane mahaifinsa ba sai Gwamnan jihar Legas.
Mista Emmanuel Sanwo-Olu yana ikirarin Mai girma Babajide Sanwo Olu ya taba samun alaka da Mahaifiyarsa shekaru da-dama da suka wuce a garinsu.
Asali: Legit.ng