Shugaban Kasa a 2023: A Karshe Tinubu Ya Yarda Zai Yi Muhawara Da Masu Neman Takara

Shugaban Kasa a 2023: A Karshe Tinubu Ya Yarda Zai Yi Muhawara Da Masu Neman Takara

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressive Congress (APC), Bola Tinubu, ya ce ba zai bari wasu suyi amfani da shi don samun kudi ba
  • Tinubu ya yi martani ne da yake amsa tambaya kan dalilin da yasa bai halarci taron Arise TV ba
  • Babban jagoran jam'iyyar mai mulki ya bayyana cewa zai iya yin muhawara daga safe har dare ba tare da tsayawa ba

Landan - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa a shirye yake don yin muhawara daga safe har dare, Daily Trusta ta rahoto.

Ku tuna cewa Tinubu ya sha caccaka bayan ya ki bayyana a muhawarar da gidan talbijin na Arise TV ya shirya wanda aka yi a ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba.

Bola Tinubu
Shugaban Kasa a 2023: A Karshe Tinubu Ya Yarda Zai Yi Muhawara Na Masu Neman Takara Hoto: OfficialABAT
Asali: Twitter

Masu suka daga jam'iyyun adawa sun zargi tsohon gwamnan na jihar Legas da guje ma muhawara da takwarorinsa.

Kasa da sa'o'i 24 bayan muhawarar Arise TV, Tinubu ya yi jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki da yan Najeriya mazauna waje a Chatham House da ke birnin Landan, kasar Birtaniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da yake jawabi a taron, Tinubu ya bayyana tanade-tanadensa gabannin zaben shugaban kasa na 2023 da kuma cewa zai fi mayar da hankali kan tsaro, tattalin arziki, ci gaban al'umma da sauran abubuwa da dama.

Na shirya muhawara daga safe har dare amma ba da wadanda zasu yi kudi dani ba, Tinubu

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, Tinubu ya yarda cewa yin muhawara da shi ba matsala bane ko kadan, ya ce:

"Na shirya yin muhawara da ku daga safe har zuwa dare...kuma ina magana ne a Landan, ba a Jigawa ba.

"Abu mai kyau ne cewa kana raye don sanar da labarin, kawai ka bayar da tabbacin cewa ba za ka cire tsammani ba...watsa shirye-shirye, karfin da kuke magana a kai..idan da sun dauki shawararmu..a farkon damokradiyya a 1999, mun kawo hannun jari. mataimakina a wancan lokacin na nan..sai kuma sabbin abubuwa..."

Kan dalilinsa na kin amsa gayyatar zuwa wajen mahawara Tinubu ya ce:

"Ina kallon kaina a matsayin mutum mai kasuwa. Kuna so kuyi amfani dani don samun kudi ni kuma ian cewa a'a."

Takalman da Peter Obi ya sa a wajen yakin neman zabensa ya haddasa cece-kuce

A wani labarin, jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar hoton yadda takalman Peter Obi suka yi fata-fata a wajen yakin neman zabensa a jihar Imo.

An dai gano takalman dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Labour Party dauke da kura wanda a cewar mutane hakan alama ce da ke nuna yana jin radadin talakawa don haka bai damu da aso ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel