Matar Atiku Ta Fadi Dalilin da Yasa Tace Yarbawa Za Su Yi Watsi da Tinubu, Su Zabi Mijinta

Matar Atiku Ta Fadi Dalilin da Yasa Tace Yarbawa Za Su Yi Watsi da Tinubu, Su Zabi Mijinta

  • Titi Atiku, matar dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ta ce, ba a taba samun Bayarbiya da ta zama uwar gidan shugaban kasa ba a Najeriya
  • Matar Atiku, wacce 'yar asalin jihar Osun ce ta bayyana hakan ne a wurin nemawa mijinta kuri'u gabanin zaben 2023 mai zuwa
  • Ta fadi hakan ne a ranar Laraba yayin kamfen dan takarar shugaban kasa na PDP da aka gudanar a birnin Akure na jihar Ondo

Akure, jihar Ondo - Titi Atiku, matar dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ta yi alkawari ga jama'ar jihar Ondo cewa, mijinta zai yaki Boko Haram sannan ya samar da tallafin karatu ga dalibai a kasar nan idan ya gaji Buhari a 2023.

Matar Atiku ta bayyana wannan alkawarin ne yayin da jam'iyyar PDP ke gudanar da taron gangamin kamfen a birnin Akure na jihar Ondo ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Jami'iyar APC Nakasu Kawai Ta Kawo A Nigeria Tsawon Lokacin da ta Shafe Tana Mulki, Atiku

Matar Atiku wacce 'yar asalin jihar Osun ce kuma Bayarbiya ta ce, babu mace daga yankin da ta taba zama uwar gidan shugaban kasa, Sahara Reporters ta ruwaito.

Matar Atiku ta ce Yarbawa ya kamata su zabi mijinta
Matar Atiku Ta Fadi Dalilin da Yasa Tace Yarbawa Za Su Yi Watsi da Tinubu, Su Zabi Mijinta | Hoto: saharareporters.com
Asali: UGC

A cewarta:

"Mutane na, ni, diyarku na tsaya a gabanku don fada muku cewa miji na ya yi abin da ya dace a baya. Miji na ne ya ci zaben da aka yi a baya amma aka yi babakere.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Tabbas miji na Bafulatani ne amma ba masheki bane muna tare da shi. Na koya masa al'adunmu, kuma ya zama danginmu.
"A lokacin Obasanjo, Atiku ne ya kawo irinsu ElRufai, Ngozi Okonjo-Iweala da sauran wadanda suka yiwa Najeriya abin kirki."

Ku zabi Atiku, ku guji Tinubu, matar Atiku ta fadi dalili

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ne babban abokin hamayyar PDP da dan takararta, kuma dan yankin Kudu maso Yamma ne.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa a 2023: Idan Na Hau Kujerar Mulki Matasa Za Su Sha Romon Dadi, Atiku Abubakar

Matar Atiku ta roki 'yan yankin Kudu maso Yamma da su yi watsi da Tinubu su zabi mijinta a zaben 2023 mai zuwa, rahoton TheCable.

Da take bayyana dalilinta, Titi ta ce:

"Babu Bayarbiyar da ta taba zama Uwar Gidan Shugaban kasa, wannan batu ne na kuri'un Yarbawa. Akwai yunwa a kasar nan, kada ku bari 'yan adawa su rude ku, ku zabi PDP daga sama har kasa."

PDP dai ta sha bayyana tanadinta ga 'yan Najeriya, tana nuna cewa ba za ta yi mulki irin na APC ba idan aka ba ta dama a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel