Tarihi Zai Maimaita Kansa, Tinubu Zai Yi Kasa-Kasa da Kwankwaso a Kano, Kwamishina

Tarihi Zai Maimaita Kansa, Tinubu Zai Yi Kasa-Kasa da Kwankwaso a Kano, Kwamishina

  • Kwamishinan labarai na jihar Kano ya yi ikirarin cewa za'a maimaita abinda ya faru a zaben shugaban kasa na 1993 a jihar
  • Muhammed Garba, yace Tinubu zai yi ƙasa-ƙasa da Kwankwaso kamar yadda Abiola ya lallasa Bashir Tofa
  • Ana gani Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iiyyar NNPP na da karfi a Kano kuma babu mai iya ja da shi

Kano - Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Muhammad Garba, ya yi hasashen cewa da yuwuwar tarihi ya sake maimaita kansa a siyasar Kano a zaɓen 2023.

Kwamishinan yace ɗan takarar shugaban kasa a APC, Bola Tinubu, zai lallasa takwaransa na NNPP kuma tsohon gwamna, Rabiu Kwankwaso, kamar yadda MKO Abiola ya yi kasa-kasa da Bashir Tofa a 1993.

Bola Tinubu da Rabiu Kwankwaso.
Tarihi Zai Maimaita Kansa, Tinubu Zai Yi Kasa-Kasa da Kwankwaso a Kano, Kwamishina Hoto: Bola Tinubu, Rabiu Kwankwaso
Asali: Facebook

Garba ya yi wannan furucin ne a wurin wata lakca da kungiyar kwararrun 'yan jarida ta shirya a Kaduna mai taken, "Mu tattauna game da Najeriya" tare da haɗin guiwar Arewa House da Hamdala Hotel.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Arewa Ya Lallaba Patakwal, Ya Sa Labule da Wike

Jaridar Vanguard ta ce Kwamishinan, tsohon shugaban ƙungiyar 'yan jarida ta ƙasa (NUJ) yace siyasa ba rubutu bane a kan duste komai zai iya faruwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kwamishinan ya ce:

"Na san tsohon gwamnan jiharnu zai shiga takardun jefa kuri'a amma tarihi zai maimaita kansa a Kano saboda Marigayi MKO Abiola na SDP ya lallasa haifaffen Kano, Bashir Tofa na jam'iyar NRC da aka rushe a zaben 1993."
"Ina da yakinin Kano zata samar da tulin kuri'u a 2023. Kuri'un dake akwai a ƙaramar hukumar Nasarawa kaɗai sun zarce na kudu maso gabashin Najeriya idan aka haɗa baki ɗaya jihohinsu."
"Ina da kwarin guiwar zamu kawo wa APC Kano Insha Allah. Gwamnatin jiha zata ba kowane ɗan takara 'yancin ya zo ya baje kolinsa kuma kowane ɗan takara zai samu kuri'u dai-dai da yadda mutane suka jefa masa."

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Kai Takararsa Zuwa Ketare, Zai Gana da Muhimman Gwamnatin Amurka

Kano ce lamba ɗaya a yawan jama'a a arewa - Garba

Muhammad Garba ya ƙara ɗa cewa jihar Kano ta fi kowace jiha yawan al'umma da zaman lafiya a arewacin Najeeiya.

The Nation ta rahoto ya ci gaba da cewa:

"Muna da tsaro a Kano kuma gwamnan mu ya baiwa kowa dama ba tare da duba addini, Ƙabila ko yare ba. Duk da kasancewarta ja gaba a yawan al'umma Kano tafi kowace jiha zaman lafiya. Arewa."

Ba Zan Zauna Gidan da Aka Lullube da Karya Ba, Jigon APC Ya Fice Daga Jam'iyyar

A wani labarin kuma Wani Babban Jigon Jam'iyyar APC a kudu maso kudancin Najeriya ya fice daga jam'iyyar

A cewarsa ba zai zauna jam'iyyar ɗa baranɓaramar sakin layi ta yi yawa ba kuma wurin da ake so ka yi karya a gaban jama'a idan an koma gida a faɗa wa juna gaskiya.

Mai neman sugabancin ƙasar nan a inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi subutar baki yayin faɗin wasu kalmomi a wuraren kamfe ɗinsa.

Kara karanta wannan

2023: APC Ta Nesanta Tinubu da Wani Hoto da Ake Yaɗawa Tare da Shugaban Amurka, Ta Faɗi Gaskiya

Asali: Legit.ng

Online view pixel