Babu Wanda Zan Baiwa Hakuru Don Na Yabi Shugaba Buhari – Gwamnan PDP

Babu Wanda Zan Baiwa Hakuru Don Na Yabi Shugaba Buhari – Gwamnan PDP

  • Gwamna Nyesom Wike ya sake jinjina wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan sakin bashin da jihohi masu arzikin man fetur ke bin FG
  • A cewar jigon na PDP, ba don kudaden ba, da bai aiwatar da duk manyan ayyukan da ya yi wa almmar jihar Ribas ba
  • Duk da wannan jinjinar da ya yi wa shugaban Najeriyan, Wike ya ce Buhari bai yi kokari ba a wasu bangarori da dama

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce babu wanda zai ba hakuri kan yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi saboda ya amince an biya jihohin Neja Delta kudaden da suke bi tun 1999.

Wike ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 3 ga watan Disamba, a wajen bikin karramawa ta jihar Ribas na 2022 wanda aka yi a Port Harcourt, babban birnin jihar, jaridar The Cable ta rahoto.

Gwamna Nyesom Wike
Babu Wanda Zan Baiwa Hakuru Don Na Yabi Shugaba Buhari – Gwamnan PDP Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

Ni ba masoyin Buhari bane amma ya yi abun da jam'iyyata ba ta yi ba, Wike

Jaridar Vanguard ta nakalto Wike yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Babu wanda zan ba hakuri. A yau, Wike ya yi wannan da wancan aikin. Duba ba don Buhari ya saki kudaden ba - daga 1999, wanda jam'iyyata bata saki ba - da ban yi abun da nayi ba.
"Ban damu da abun da kowa zai fadi ba. Ban damu ba. Na samu kudaden. Ni ba masoyin Buhari bane. Bai yi kokari ba a wurare da dama amma wajen biyan kudaden nan, ya yi kokari.
"Ba lallai ne abokaina da 'ya'yan jam'iyyata su ji dadi ba. Kada ku yi fushi faaa. A wannan, Buhari ya yi kokari. Ya bani kudin kuma na yi amfani da shi wajen yiwa mutanen jihar Ribas wani abu. Sauran zasu yi maganar nasu daga baya."

Idan mutum ya yi abun a yaba masa toh ka fada, idan yayi akasin haka shima ka fada, Wike

Ku tuna cewa a ranar 18 ga watan Nuwamba, Wike ya sanda da cewar gwamnatin Buhari ta biya jiharsa da sauran jihohin Neja Delta kudaden da suke bin gwamnatin tarayya.

A cewar Wike, kudaden da gwamnatin tarayya ta biya ya taimaka masa sosai wajen yiwa jiharsa abubuwan more rayuwa.

Amma gwamnan na jihar Ribas ya ce yanzu haka yana fama da matsala saboda ya yaba ma Buhari kan amincewa da mayarwa jihohin masu arzikin man fetur kudaden da ya yi.

Ya kara da cewar:

"Maimakon mutane su ce sun gode maka, sai su koma bakin ciki cewa me yasa aka yaba maka. Saboda na ce Buhari nagode, ina samun matsala a yau.
"Ni ba masoyin Buhari bane. Na fada ma mai girma atoni jamar amma idan mutum yayi kokari ka fada cewa ya yi kokari a wannan bangaren. a daya bangaren da bai yi kokari ba, shima sai ka fadi."

Gwamna Wike ya ce Buhari ya biya jihohin Neja Delta kason da suke bi na rarar mai

A baya mun ji cewa Gwamna Nyesom Wike ya tabbatar da cewar lallai gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta dawo wa jihohin Neja Delta kudaden da suke bin ta.

Hakan ya biyo bayan taso gwamnonin da mutane suka yi a gaba kan su yi bayanin abun da suka yi da kason da suka samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel