2023: Jerin Jihohin Arewa 6 da Manyan Jam'iyyu APC Da PDP Zasu Fafata Kan Kuri'u 12.8m

2023: Jerin Jihohin Arewa 6 da Manyan Jam'iyyu APC Da PDP Zasu Fafata Kan Kuri'u 12.8m

Ayyana Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban kasa na PDP da Kashim Shettima a matsayin abokin tarakarar Tinubu na APC ya maida arewa maso gabas fagen da fafatawa zata zafafa a 2023.

Atiku, tsohon mataimakin shugaban kasa daga jihar Adamawa zai nemi lashe kuri'u miliyan 12.8m da yankin suka yi rijistar kaɗa wa kan tsohon gwamnan Borno, Shettima.

A dai-dai lokacin da 'yan Najeriya ke fuskantar babban zaben 2023 a watan Fabrairu, 2023, ana ganin fafatawa zata yi dumi tsakanin PDP da APC a shiyyar arewa maso gabas.

Manyan 'yan takara biyu dake sahun gaba.
2023: Jerin Jihohin Arewa 6 da Manyan Jam'iyyu APC Da PDP Zasu Fafata Kan Kuri'u 12.8m Hoto: Atiku Abubakar, Bola Tinubu
Asali: Facebook

Legit.ng Hausa ra fahimci cewa idan APC ko PDP suka lashe zaɓen 2023 mai zuwa, shiyyar zata samar da mataimakin shugaban ƙasa a karo na 2, ko kuma shugaban ƙasa a karon farko.

Jihohi 6 dake yankin sun haɗa da;

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Ya Ja Wa Kansa, Wani Babban Jigon APC Ya Fice Daga Jam'iyyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Borno

2. Yobe

3. Bauchi

4. Taraba

5. Adamawa

6. Gombe

Waɗannan jihohin zasu zama fagen da zabe zai yi zafi a tsakanin manyan jam'iyyu biyu watau APC da PDP.

Borno

Mai yuwuwa jihar Borno ta zama mai saukin samun nasara ga jam'iyyar APC saboda ita ke rike da madafun iko karkashin gwamna Babagana Zulum.

A cewar INEC, Borno na da masu kaɗa kuri'a 2, 315, 956 kuma Shettima, tsohon gwamnan jihar ka iya tattara mafi yawan kuri'un ga jam'iyyarsa watau APC.

Yobe

Yobe, jiha ta biyu kenan dake karkashin mulkin APC. Mutane miliyan 1,365, 913 ne suka yi rijistar zabe inji INEC.

A ko da yaushe APC ke samun nasara a Yobe amma ana hasashen taƙaddamar da ke wakana a jam'iyyar kan abinda wasu suka kira, "Kakaba yan takara" ka iya jawo naƙasu ga jam'iyyar a 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Arewa Ya Lallaba Patakwal, Ya Sa Labule da Wike

Bauchi

Wannan jihar PDP ce mai ƙunshe da masu kaɗa kuri'a sama da Miliyan 2.4m, wanda ake tsammanin da daɗi ko ba daɗi Atiku, zai yi kokarin lashe su.

Amma akwai matsala tsakanin gwamna Bala Muhammed na Bauchi da Atiku Abubakar kuma a kwanan nan an ji Kauran Bauchi na cewa mutanen jihar 'yan Buhariyya ne.

Taraba

Taraba ta jima a matsayin sansanin goyon bayan Atiku amma da yuwuwar wasan ya canza salo a 2023 biyo bayan rigimar data shiga tsakanin Sanata Samuel Bwacha da gwamna mai ci, Darius Ishaku.

A kwanan nan aka tabbatar da halascin Bwacha a matsayin ɗan takarar gwamna a Inuwar APC. Saboda haka zaɓen shugaban ƙasa zai ba da citta a tsakanin APC da PDP.

Adamawa

Mahaifar Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, mai mutane masu katin zaɓe sama da miliyan 1.7m.

Ana ganin cikin ruwan sanyi Atiku zai lashe jihar amma nasarar Aishatu Binani a matsayin 'yar takarar gwamna a inuwar APC ya zama babbar barazana.

Kara karanta wannan

2023: Dubbannin Mambobin Jam'iyyun PDP da LP Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Arewa

Sanata Binani ta samu nasara a zaɓen fidda gwanin APC bayan lallasa tsohon gwamna, Jibrilla Bindow da tsohon shugaban hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribado.

Gombe

Ta karshe jihar Gombe wacce APC ke jan ragamarta tana da masu kaɗa kuri'a sama da miliyan 1.3m.

Maslahar da aka samu a kwanan nan tsakanin Sanata Danjuma Goje da gwamna Inuwa Yahaya ta ƙarawa APC damar nasara sama da PDP.

A wani labarin kuma Abokin Gamin Atiku, Tambuwal Da Wasu Jga-Jigan PDP Sun Lallaba Gidan Tsohon Shugaban Kasa

Duk da babu cikakken bayani kan abinda ya kai su da muhimman abubuwan da suka tattauna ana ganin ziyarar ba zata rasa alaƙa da rikicin jam'iyyar PDP ba.

Gwamna Aminu Tambuwal, Darakta Janar na kamfen Atiku, yace sun je gaida tsohon shugaban ne kuma ya roki 'yan Najeriya su mara wa Atiku/Okowa baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262