Wike Ya Rabu da Atiku da Ayu, Ya Koma Kan Gwamnoni 5, Ya Jefa Masu Kalubale

Wike Ya Rabu da Atiku da Ayu, Ya Koma Kan Gwamnoni 5, Ya Jefa Masu Kalubale

  • Nyesom Wike ya caccaki wadanda suke sukarsa saboda ya yi Shugaban kasa Muhammadu Buhari godiya
  • Gwamnan Ribas ya yabawa Gwamnatin Buhari a dalilin wasu bashin kudi da ya biya jihohin Neja-Delta
  • Wike yace da wadannan kudi ya yi wa mutanensa aiki, ya jefa kalubale ga sauran abokan aikinsa a Kudu

Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya sake waiwayan Gwamnonin Neja-Delta a game da bashin kudin da gwamnatin tarayya ta biya su.

The Nation ta rahoto Mai girma Nyesom Wike yana kira ga gwamnonin Neja-Delta su daina sukarsa saboda kurum ya yabawa Muhammadu Buhari.

Gwamnan yake cewa a maimakon haka, abokan aikinsa su dauki makonni uku suna kaddamar da ayyukan da suka yi wa jihohinsu, kamar yadda ya yi.

Wike ya fito yana cewa ana labewa da sunan wasu kungiyoyi domin a soke shi, ya yi kira ga masu yin wannan da su cire tsoro su tunkare shi da kyau.

Kara karanta wannan

Daya Bayan Daya, Gwamnoni Suna Maidawa Buhari Martanin Zargin da Yayi Masu

Al'ummar Ribas na ganin ayyuka

Jaridar tace Wike ya yi wannan magana ne a lokacin da yake kaddamar da titin farko da aka yi wa mutanen Rumuodogo a karamar hukumar Emohua.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ji Gwamnan na Ribas yana cewa bai taba yin kwangilar da ta wuce shekara daya da rabi ba, yace yana aiki ne saboda Rotimi Amaechi ya yi masa gori.

Nyesom Wike
Gwamna Nyesom Wike da Babajide Sanwo Olu Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Cikin cika-bakin da Gwamnan ya yi shi ne, ya yi ikirarin samun mulki ba tare da uban gida ba, yace sauran gwamnoni na da wadanda suka tsaya masu.

Laifin da nayi wa Neja-Delta - Wike

“Menene laifi na yau a Jihohin Neja-Delta? Nace mun godewa Allah da Shugaba Buhari ya ba ni kudin yin titin nan.
Nayi wani laifi? Ban san laifin da nayi saboda nayi godiya ba.
Bari in fadawa masu yin surutu. Ko kai Gwamnan jiha ne, babu ruwana. Ko wanene kai, babu wani abin da ya dame ni.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Babbar Mota Ta Murkushe Motocin Ayarin Gwamnan Arewa, Ya Sha Da Kyar

Na zo nayi takarar Gwamna ni kadai. Muka doke Gwamna mai-ci. Wasu Gwamnonin iyayen gida suka kawo su mulki.
Ban taba samun wani Ubangida ba, Ubangidan da nake da shi a Ribas shi ne Ubangiji da kuma mutanen jihar nan.”

- Nyesom Wike

An ji labari Muhammadu Buhari ya yi wa Gwamnoni kudin goro, yace suna taba kudin kananan hukumomi, wasu sun fara fitowa domin nesanta kansu daga zargin.

Gwamna David Umahi, Solomon Lalong, da Nyesom Wike da wasu Gwamnonin jihohi masu-ci, sun nuna babu ruwansu da baitul-malin kananan hukumomin na su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel