Takarar Peter Obi Ta Gamu da Cikas a Hanya, Jam'iyyar LP ta Kori Shugaban Kamfe
- Doyin Okupe ya samu kan shi a matsala bayan Shugabannin jam’iyyar LP na Ogun sun kore shi
- An fatattaki Dr. Okupe da wasu mutane 10 daga LP saboda rashin biyan kudin rajista na wata-wata
- A halin yanzu Okupe shi ne Shugaban kwamitin yakin neman zaben Shugaban kas ana Peter Obi a 2023
Ogun - Shugabannin jam’iyyar LP na reshen jihar Ogun, sun kori Darekta Janar na kwamitin yakin neman zaben Peter Obi - Datti, Doyin Okupe.
Vanguard ta kawo rahoto a ranar Alhamis, 1 ga watan Disamba 2022 cewa an kori Dr. Doyin Okupe da wasu mutum 10 daga jam’iyyar adawar a Ogun.
Shugabannin LP sun dauki wannan matsaya ne a garin Abeokuta, ana zargin wadannan ‘ya ‘ya da aka kora da rashin biyan kudin wata-wata.
Kamar yadda shugaban LP da sakatarensa na Jiha; Michael Ashade da Feyisola Michael suka bayyana, kin biyan kudin jam’iyya ya sabawa doka.
Wadanda aka kora daga LP
Wadanda aka sallama daga jam’iyyar sun hada da Abayomi Collins, Abel Olaleye, Jagun Lookman, Olori Oluwabukola Soyoye, da Gbadebo Fesomade.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akwai Abdulmalik Olaleye, Jide Amusan, Adeshina Wasiu Shojobi, Deborah Adewale da Olatunde Abolade duk a cikin wadanda aka kora daga jam’iyyar.
Michael Ashade ya kalubalanci Okupe ya fito da hujjar da ke nuna cewa ya taba biyan kudin zama ‘dan jam’iyya a banki kafin 1 ga watan Disamban 2022.
Peter Obi bai da DG?
Rahoton yace Ashade ya nemi shugaban LP na kasa, Barr. Julius Abure ya cire Okupe daga matsayin da yake kai na Darekta Janar na yakin zaben Obi.
An bukaci a nada sabon DG daga Arewacin Najeriya domin ayi adalci. A dokar jam’iyya, wanda ba ya biyan kudin wata-wata ba zai rike mukami ba.
Ba gaskiya ba ne Inji Shugaban Jam'iyya
Ana haka sai aka ji Punch ta rahoto shugaban LP na kasa, Julius Abure yana musanya labarin korar Okupe da wasu jagorori daga jam’iyyarsu.
Abure yace labarin bogi ake yadawa, ya kuma shaidawa manema labarai shugabannin jiha ba su da ikon tsige Darektan yakin zaben shugaban kasa.
Kwankwaso yana Amurka
Dazu aka ji labari ‘Dan takaran Shugaban Kasa a NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso PhD ya yi koyi da irinsu Atiku Abubakar da Peter Obi wajen tafiya Amurka.
Rabiu Musa Kwankwaso mai neman shugabancin Najeriya a jam’iyyar NNPP a 2023 yana tallata kwandon kayan dadi a Amurka bayan ya baro Faransa.
Asali: Legit.ng