PDP Ta Sha Alwashin Yi Wa Gwamnan Babban Jihar Arewa Ritaya Zuwa Saudiyya A 2023

PDP Ta Sha Alwashin Yi Wa Gwamnan Babban Jihar Arewa Ritaya Zuwa Saudiyya A 2023

  • Babban Jam'iyyar hamayya ta PDP, a jihar Nasarawa da ke arewa maso tsakiya a Najeriya ta ce zata yiwa Gwamna Abdullahi Sule ritaya zuwa kasa mai tsarki wato Saudiyya
  • Ciyaman din PDP a jihar ta Nasarawa, Mr Francis Orogu ne ya sanar da hakan yayin wata zantawa da ya yi da yan jarida a ranar Alhamis a karamar hukumar Karu
  • Orogu ya ce Sule ya nuna cewa ba zai iya jan ragamar jihar ba don hakan za su yi masa ritaya na dole zuwa kasar Saudiyya kuma ba su tsoron barazanar da ya ke musu

Jihar Nasarawa - Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP a jihar Nasarawa ta yi alkawarin aike wa da Injiniya Abdullahi Sule zuwa Saudiyya a 2023, Daily Trust ta rahoto.

Mr Francis Orogu, ciyaman din jam'iyyar PDP na jihar, ne ya sanar ha dakan ne yayin hira da yan jarida a ranar Alhamis 24 ga watan Nuwamba, a karamar hukumar Karu.

Kara karanta wannan

Alkawari kaya: Tinubu ya fadi yadda zai yi da 'yan IPOB idan ya gaji Buhari a 2023

Abdullahi Sule
PDP Ta Sha Alwashin Yi Wa Gwamnan Babban Jihar Arewa Ritaya Zuwa Saudiyya A 2023. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Nigerian Tribune ta rahoto cewa Orogu yana zargin cewa gwamnan ya nuna cewa ba zai iya mulkar jihar ba yana mai alfaharin cewa PDP za ta fatttake shi zuwa Saudiyya idan wa'adin sa na farko ya zo karshe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalamansa:

"Jam'iyyar APC bisa la'akari da dukkan alkalluma ta gaza, don haka zaben mai zuwa abu mai sauki ne ga PDP. A shekarar 2023, za mu kore shi zuwa Saudiyya."

Mr Orogu ya soki gwamnan kan zarginsa da shan alkawarin kawar da duk wanda zai shiga tsakaninsa da kai wa ga kujerar gwamna yayin da ake tunkarar zaben 2023, ya kuma nanata cewa PDP ba zata tsorata ba.

Duk da haka, ya yi gargadin cewa jam'iyyar hamayya za ta bijirewa duk wani barazana da jam'iyyar mai mulki ta yi ta hanyoyin da suka dace, yayin da ya bukaci masu zabe su tabbatar an kirga kuri'unsu.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Dan Takarar Gwamna Mai Karfi A Jihar Arewa Ya Bayyana Shirinsa Na Karɓe Mulki Daga Hannun APC

Tunda fari, Dr Ombugadu David, yayi kira ga shugabanni su kaurace wa tada zaune tsaye.

Ya ce PDP ba zata durkusa zuwa matakin jam'iyyar ta APC mai mulki a jihar ba ba, inda ya ce jam'iyyar za ta bada himma kan yadda zata kawo cigaban kasa.

Gwamnan Jihar Nasarawa Ya Bayyana Yawan Shekarun Da Tinubu Zai Yi Kan Mulki Bayan Buhari

A wani rahaton, gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai mulki Najeriya tsawon shekaru takwas.

Daily Trust ta rahoto cewa ya kuma ce babu dalilin kwatantan dan Mr Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party.

Gwamna Sule ya sanar hakan ne yayin tattaunawa da aka yi da shi cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV.

Asali: Legit.ng

Online view pixel