Zan Tattauna Da ’Yan IPOB da Duk ’Yan Awaren Kasar Nan, Inji Bola Ahmad Tinubu

Zan Tattauna Da ’Yan IPOB da Duk ’Yan Awaren Kasar Nan, Inji Bola Ahmad Tinubu

  • Tsohon gwamnan Legas kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya bayyana manufarsa ta tattaunawa da 'yan aware
  • Bola Ahmad Tinubu ya ziyarci jihar Ebonyi domin kaddamar da kamfen din takarar shugaban kasa na APC a jihar
  • Ya yi alkawarin kawo hanyoyin ci gaba ga yankunan Kudu maso Gabas matukar suka ba shi damar gaje Buhari a 2023

Abakaliki, jihar Ebonyi - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya ce idan aka zabe shi ya gaji Buhari a 2023 zai bude kofar tattaunawa da 'yan aware, ciki har da IPOB, Daily Trust ta ruwaito

IPOB dai wata haramtacciyar kungiya ce ta ta'addanci mai aikata ayyukan ta'addanci tare da barnata dukiyoyi da kadarorin gwamnati a yankunan Kudu maso Gabas.

Kungiyoyin aware ba su da burin da ya wuce su samu damar ballewa daga Najeriya saboda rashin imani da turbar da kasar ke kai.

Kara karanta wannan

2023: APC ta samu karin karfi, wasu jiga-jigan sarakuna sun ce suna goyon bayan Tinubu

Tinubu ya yi alkawarin tattaunawa da IPOB
Zan Tattauna Da ’Yan IPOB da Duk ’Yan Awaren Kasar Nan, Inji Bola Ahmad Tinubu | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Da yake magana a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi yayin kamfen din APC a ranar Alhamis, Tinubu ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Muna son zaman lafiya, za mu tattauna da 'yan aware, wannan abin ba da tashin hankali ake yinsa ba."

Ba wannan ne karon farko da Tinubu yace zai tattauna da 'yan aware ba, ya fadi hakan a makon jiya yayin da ya kai ziyara jihar Imo, The Nation ta ruwaito.

Zan yi ayyukan gyara hanyoyi a kasar nan

Ya kuma bayyana cewa, zai ci gaba da ayyukan gyara da gina hanyoyi a kasar nan, musamman a fannin layin dogo da gwamnatin Buhari ta fara.

Tsohon gwamnan na Legas ya ce, aikin gyara da ginin da zai yi zai samar da layin dogo daga Calabar zuwa yankin Kudu maso Gabas

Kara karanta wannan

2023: Dan majalisa a APC ya ba 'yan Najeriya wata shawara kan zaban Tinubu

Ya kuma yi alkawari inganta fannin ilimi da wutar lantarki domin inganta rayuwar 'yan Najeriya.

A cewarsa:

"Babu hanya mai hannu biyu daga Ebonyi zuwa Enugu. Ina farin cikin kasancewa a cikinku. Kuma, sufuri dole ne idan ana magana kan tafiyar tattalin arziki da ci gabansa. Za mu ci gaba da aikin layin dogo duk da kuwa suna sace kayayyakin aiki."

A tun farko, gwamnan da ya tarbi Tinubu a jihar Ebonyi, David Umahi ya bayyana cewa, yankun Kudu maso Gabas ya samu tagomashi daga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

A cewarsa:

"Saboda haka, mu masu biyayya ne ga APC."

Rahotanni na bayyana cewa, akwai yiwuwar Bola Tinubu ya rasa kuri'u a yankun Kudu maso Yamma, saboda tuni 'yan yankin suka nuna kauna ga dan takarar jam'iyyar Labour, Peter Obi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.