Labari Mai Dadi Ga APC, Tinubu Ya Samu Babban Goyon Baya a Yankin Su Peter Obi

Labari Mai Dadi Ga APC, Tinubu Ya Samu Babban Goyon Baya a Yankin Su Peter Obi

  • Bola Ahmad Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC na ci gaba da samun karbuwa a yankin Kudancin kasar nan
  • A baya ana tunanin 'yankin Kudu maso Gabas ne zai iya yiwa Tinubu wahala a zaben 2023, amma ya samu karbuwa
  • A yanzu, sarakunan gargajiya da masu fada a ji a jihar Ebonyi sun bayyana goyon bayansu gareshi, amma da sharadi

Jihar Ebonyi - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya samu karbuwa mai kyau yayin da zaben 2023 ke kara karatowa, The Nation ta ruwaito.

Tinubu a baya dai bai samu karbuwa da goyon bayan jama'ar yankin Kudu maso Gabas ba, amma a yanzu ya samu babbar tarba a hannun sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki a jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

"Mazi Tinubu": Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar APC Ya Samu Sarauata A Yankin Su Peter Obi

Kamar yadda rahoto ya bayyana, sarakunan gargajiya a jihar Ebonyi sun tattauna da Tinubu a ranar Laraba 23 ga watan Nuwamba, kuma sun yi alkawari ba shi goyon baya a aniyarsa ta gaje Buhari.

Shugaban majalisar sarakunan gargajiya na jihar, Eze Charles Mkupuma ya shaidawa Jagaban cewa, ya yanke kawai ya yi nasara, saboda suna goyon bayansa.

Dan takarar shugaban kasan APC, Tinubu ya samu karbuwa a idon sarakunan Kudu maso Gabas
Labari Mai Dadi Ga APC, Tinubu Ya Samu Babban Goyon Baya a Yankin Su Peter Obi | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalaman Mkpuma:

"Muna taya shugaban kasanmu na gaba, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu murna a nasarar da ka samu a zaben fidda gwanin shugaban kasa da aka kammala.
"Mutanenmu na farin ciki da cewa ka zo nan don ganinmu duk da cewa mun yanke shawarin ba ka goyon baya da sauran 'yan takarar jam'iyyar APC."

Ka ba mu kujerar shugaban majalisar dattawa

A bangare guda, Mkpuma ya roki Tinubu da ya tuna da yankin idan ya gaji Buhari, ya dauki dan jihar Ebonyi ya bashi kujerar shugaban majalisar dattawa bayan ya ci zabe, Daily Independent ta tattaro.

Kara karanta wannan

2023: Dan majalisa a APC ya ba 'yan Najeriya wata shawara kan zaban Tinubu

Legit.ng ta tattaro cewa, dan takarar shugaban kasan na APC ya dura Kudu maso Gabas ne don kaddamar da kamfen dinsa a birnin Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.

Masu sharhi kan siyasar kasar nan sun yi imani da cewa, jihohin Kudu maso Gabas za su iya goyon bayan Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, amma an saba lamba.

Duk da wannan goyon bayan da Tinubu ke samu, akwai jihohi 5 da watakila ya samu matsala duk da kuwa jihohi ne na APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.