Kwara, Imo da Wasu Jihohi 2 Na APC da Tinubu Ka Iya Rasa Kuri'unsu a Zaben 2023

Kwara, Imo da Wasu Jihohi 2 Na APC da Tinubu Ka Iya Rasa Kuri'unsu a Zaben 2023

  • Jam'iyyar APC mai mulki na kokarin ganin ta ci gaba da mukar Najeriya har gaban 2023 a matakin shugaban kasa a Najeriya
  • Jam'iyyar mai mulki na da wasu damammaki, da suka hada da tarin gwamnoni da ke da karfin iko a jihohin kasar nan
  • Sai dai, akwai yiwuwar a samu tasgaro a tafiyar Tinubu, domin zai iya rasa kuri'un wasu jihohin APC saboda wasu dalilai

Duk da cewa al'adace a Najeriya dan takarar shugaban kasa a jam'iyya ya ci zabe a jihohin da jam'iyyarsa ke mulki, akwai yiwuwar samun sabanin haka a zaben 2023 mai zuwa.

Saboda dalilai guda biyu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ba lallai ya ci zabe a wasu jihohin ba duk da kuwa gwamnonin 'yan APC ne.

Jihohin da Tinubu zai iya cin dungure idan bai kula ba
Kwara, Imo da Wasu Jihohi 2 Na APC da Tinubu Ka Iya Rasa Kuri'unsu a Zaben 2023 | Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Jihohin da ake magana a kai sun hada da:

Kara karanta wannan

Zaɓen Shugaban Ƙasa: Jihohin PDP 7 Masu Ƙarfi Da Atiku Zai Iya Shan Kaye A 2023

  1. Kuros Riba
  2. Ebonyi
  3. Imo
  4. Kwara
  5. Ogun

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rikicin cikin gida da batutuwan da suka shafi Kudu maso Gabas

A 2019, shugaba Muhammadu Buhari ya rasa kuri'un wasu jihohin saboda wasu rikice-rikicen cikin gida a jam'iyyar APC.

Bata sauya zane ba, watanni kadan da suka gabata, shugaban APC na kasa, Adamu Abdullahi ya ta'allaka rasa nasarar da APC ta yi a zaben 2022 na jihar Osun da rikicin cikin gida.

Watanni kadan gabanin zaben 2023, yanzu haka APC na fuskantar zazzafan rikicin cikin gida akalla a jihohi uku da take mulka; Kuros Riba, Kwara da Ogun.

Rikicin APC a jihar Kuros Riba

Zaben fidda gwanin gwamnan APC a jihar Kuros Riba ya kasance cikin rikici yayin da Owan Enoh ke kalubalantar nasarar Sanata Bassey Edet Otu.

Duk da cewa kotu ta tabbatar da nasarar Otu, wannan lamari na ci gaba da dagula APC a jihar ta Kudu maso Kudu.

Kara karanta wannan

Tinubu: Buhari ya jefa Najeriya a yunwa, amma ya yi wani abu 1 da ya kamat kowa ya sani

A baya-bayan nan wani jigon APC a jihar, Sam Bassey ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar gwamnan PDP, Sandy Onor a jihar.

Idan baku manta ba, Kuros Riba ta zama jihar APC ce yayin da gwamna Ben Ayade ya bayyana sauya sheka zuwa jam'iyyar.

Wannan lamari mai tsami a jihar ka iya jawowa Tinubu matsala a zaben 2023 mai zuwa.

Rikicin APC a jihar Ogun

Haka lamarin yake a jihar Osun, inda sanata mai ci kuma tsohon gwamna Ibikunle Amosun ke cikin dambarwar rikici da magajinsa gwamna Dapo Abiodun.

Amosun na goyon bayan dan takarar shugaban kasa na APC, Tinubu amma ya bayyana yin watsi da tafiyar Abiodun.

Idan APC bata kula ba, wannan na iya zama tasgaro ga Bola Tinubu a zaben 2023 mai zuwa, duk da kuwa PDP a jihar na fuskantar rikici tare da jiga-jiganta da Atiku, dan takarar shugaban kasa na PDP.

Kara karanta wannan

Ganduje: Kwankwaso Bashi da Karfi Yanzu, Ba zai Kai Labari ba a 2023

Rikicin Lai Mohammed da gwamna AbdulRahman AbdulRazaq a jihar Kwara

A jihar Kwara kuwa, sansanin APC ya rabe gida biyu; tsagin gwamna mai ci AbdulRahman AbdulRazaq da ministan yada labarai Lai Mohammed.

Idan wannan rikici bai warware ba har zuwa zaben 2023, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki na iya illata APC tare da kawo kuri'u ga PDP a jihar da ke Arewa ta Tsakiya.

Rikicin APC a jihar Imo

Yankin Kudu maso Gabas ba yanki ne da ke kaunar APC. Tun 1999, yankin Inyamurai ya zama yankin da ya karbi tafiyar PDP hannu bibbiyu.

A zaben 2023, suna da zabi biyu; ko da su bi tafiyar Atiku a PDP ko kuma su tafi kan turbar jam'iyyar Labour ta su Peter Obi wanda kuma shi dan yankin ne.

Saboda haka, duk da cewa gwamnonin Imo da Eboyni 'yan APC ne, to akwai yiwuwar Tinubu ya rasa kuri'un jihohin saboda Peter Obi ya samu karbuwa sosai a can.

Kara karanta wannan

Matasan Jihar Buhari Sun Fara Zuwa Gida-Gida, Sun Yi Wa Tinubu Alkawarin Kuri'u Miliyan a 2023

Duk da rikicin da APC ke fuskanta, dan majalisa ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa, Tinubu ba zai ba 'yan kasar kunya ba idan ya gaji Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.