An Tsare Jirgin ‘Dan Takaran Shugaban Kasa Yana Daf da Yin Gagarumin Taron Kamfe

An Tsare Jirgin ‘Dan Takaran Shugaban Kasa Yana Daf da Yin Gagarumin Taron Kamfe

  • Hukuma ta rike jirgin saman da Peter Obi da mutanensa suke amfani da shi wajen yawon yin kamfe
  • An tsare jirgin da sunan aiki, amma hakan bai kawowa tafiyar Obidients cikas wajen yakin zabe ba
  • A wani jawabi da ya fito ta ofishin Diran Onifade, an ji cewa tsare jirgin bai hana ayi taron Ibadan ba

Abuja - Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar LP, ya yi ikirarin an tsare masa jirgin saman da yayi niyyar amfani da shi.

The Cable ta rahoto kwamitin yakin neman zaben LP a 2023 yana zargin masu mulki da rike jirgin saman da suka nemi su je jihar Oyo a cikin sa.

Peter Obi da ‘yan tawagarsa suna kan hanyar zuwa Ibadan a jihar Oyo ne wannan lamarin ya auku a filin tashi da saukan jirgin garin Abuja.

Kara karanta wannan

Shugabbanin Kudu Sun Koka Kan Yadda Aka Maida su saniyar Ware Musamman A Faggen Shugabancin

Shugaban sashen yada labarai na kwamitin, Diran Onifade ya fitar da jawabi a ranar Larabar nan, yace an karbe masu jirgi da sunan ka’idar aiki.

Jawabin Diran Onifade

Diran Onifade ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar LP suyi watsi da rade-radin da wasu ke yadawa na cewa an karbe jirgin saman gaba daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da abin da ya faru, Kakakin kwamitin neman zaben ya shaida cewa jam’iyyar LP za ta gudanar da taron siyasar da tayi niyya a garin Ibadan.

Jirgin sama
Jirgin saman Obidient Hoto: sundiatapost.com
Asali: UGC
“An tsare jigin saman ‘Yan Obidient ta hannun masu rike da madafan iko da sunan “ka’idar aiki” kurum.
Kuyi watsi da duk wata muguwar jita-jitar da ake yadawa. Za ayi babban taronmu kamar yadda aka tsara.”

- Diran Onifade

A shiryawa gangamin Oyo - Obi

A daf da hakan za ta faru, Peter Obi ya yi magana a shafinsa na Twitter, ya yi kira ga mabiyansa da su shiryawa babban gangamin da za ayi a jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Binciken ‘Yan Sanda Ya Nuna Jihohi 2 da Za a fi Samun Tashin Hankali a Zaben 2023

Masu fashin bakin siyasa suna ganin cewa Oyo da sauran jihohin Kudu maso yammacin Najeriya suna cikin wuraren da APC take da karfi a siyasa.

Duk da cewa ‘dan takaran jam’iyya mai mulki watau Bola Tinubu ya fito daga yankin ne, da alama Peter Obi da jam’iyyarsa za su samu kuri’u a zaben 2023.

Sabanin GEJ da Atiku a 2015

An samu labari ashe tun daga Abuja, Goodluck Jonathan yana kan kujerar Shugaban kasa ya je Landan domin ya shawo kan Atiku Abubakar ya dawo PDP.

Yadda Atiku Abubakar ya ki yarda ya goyi bayan PDP a 2015, haka Gwamna Nyesom Wike da mutanensa suke yakar PDP a zaben da za ayi a shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng