Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari Ya Raba Jaha da Tinubu, Yace Atiku Zai Goya Wa Baya a 2023

Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari Ya Raba Jaha da Tinubu, Yace Atiku Zai Goya Wa Baya a 2023

  • Taohon Sakataren gwamnatin shugaba Buhari, Babachir Lawal, yace sun raba gari da Tinubu saboda tikitin Musulmi da Musulmi
  • Babachir yace ba zai taimaka wa Tinubu a 2023 ba kuma ya kulla yarjejeniya da PDP ɗan takararta zai wa aiki a 2023
  • Tsohon SGF yace bai damu da duk abinda za'a ce ba amma shi da magoya bayansa ba zasu zabi APC ba

Tsohon Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, yace jam'iyyarsa APC zata sha ƙasa a zaɓen shugaban kasa na 2023 sakamakon tikitin Musulmi da Musulmi.

A wata hira da BBC, Babachir Lawal, Jigon jam'iyyar APC yace da taimakonsa da wasu ɗan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya lashe zaɓen fidda gwani.

Babachir Lawal.
Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari Ya Raba Jaha da Tinubu, Yace Atiku Zai Goya Wa Baya a 2023 Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Amma a cewarsa daga baya suka gano cewa yana da wata ɓoyayyar manufa ta zakulo Musulmi ɗan uwansa a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaba.

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi da Musulmi: Tinubu Da Shettima Ba Za Su Dandana Mulkin Najeriya Ba a 2023, inji Babachir Lawal

Babachir yace ya daina goyon bayan Bola Tinubu kuma jam'iyyar APC ba zata kai ko ina ba a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa yace, "Mun raba jaha da Bola Tinubu yanzu, ba ruwana da tikitin Musulmi da Musulmi."

"Bola da kansa ya nuna baya son tafiya damu, ya zaɓi inda yake son zuwa kuma mun riga da mun faɗa masa zai rasa kuri'unmu idan ya tsaida Musulmi ɗan uwansa."

Wane ɗan takara tsohon SGF zai mara wa baya a 2023?

"Mun tattauna da jam'iyyar PDP kuma sun amince da bukatunmu idan muka goya musu baya kuma mun yarda zamu kaɗa musu kuri'unmu."

- Babachir Lawal.

Jam'iyyar PDP ta haɗa Tikitin Musulmi da Kirista, Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa da kuma gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa.

Kara karanta wannan

Duk Wanda Yace 2023 Lokacinsa ne, Ya Tafka Babban Kuskure, Kwankwaso Yayi Gugar Zana

Tsohon SGF ya ƙara da cewa tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, ya yi iya bakin kokarinsa na jawo ra'ayinsa da sauran mambobin APC da suka fusata amma bai kai ga nasara ba.

Shin akwai yuwuwar sasantawa da Tinubu?

Yayin da aka tambaye shi ko zai nemi Tinubu su zauna kan batun, Babachir yace, "Aa, shi ne zai neme mu a yanzu, ni dai ba zan je wurinsa ba. Ya san inda muke amma bai neme mu ba."

Ya ƙara jaddada cewa yana nan daram a cikin jam'iyyar APC amma shi da magoya bayansa ba zasu mara wa Bola Tinubu baya ba.

Game da yuwuwar za'a zarge shi da kokarin yi wa jam'iyya zagon ƙasa, Tsohon Sakataren yace bai damu ba ko da kuwa za'a zage shi.

"Da zaran Buhari ya jingine siyasa nima zai take masa baya saboda na tsunduma siyasa ne domin shi," inji Babachir.

Kara karanta wannan

Hotunan Yadda Manyan 'Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu Suka Tara Jama'a Ba Masaka Tsinke a Jiha Ɗaya

A wani labarin kuma Kalaman da Kwankwaso ya yi a jihar Ribas kan ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP sun bar baya da ƙura

Tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma makusancin Atiku, Mista Chidoka, ya ce ga dukkan almau lissafin Kwankwaso ya kwace game da zabe a Najeriya.

A cewarsa tunda mulkim Dimokuraɗiyya ya dawo babu jam'iyyar da ta lashe jihohi uku da Kwankwaos ke ta da jijiyoyin wuya a kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel