Rikicin PDP: Gwamnan APC Ya Shiga Kungiyar Gwamnonin G5, Ya Dinke Da Wike
- Gwamna Dave Umahi ya yanki lasisin kungiyar gwamnonin G-5 na PDP inda suka koma G-6 a yanzu
- Gwamnan na jihar Ebonyi ya sanar da shigarsa kungiyar a jihar Ribas na a ranar Talata, 22 ga watan Nuwamba
- Umahi ya ce yana bayan Gwamna Nyesom Wike dari bisa dari a wannan gwagwarmaya tasa saboda hakan zai amfani Najeriya sosai
Rivers - Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi kuma babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya ce shima ya zaman mamba a kungiyar gwamnonin G5 (gwamnonin PDP biyar), rahotom TheCable.
Kungiyar G5 ta bayyana ne yayin da ake tsaka da rikici a cikin jam’iyyar PDP kan neman Iyorchia Ayu ya sauka daga matsayin shugaban babbar jam’iyyar adawar na kasa.
Kungiyar G5 wacce ts kunshi Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, Seyi Makinde na Oyo, Okezie Ikpeazu na Abia, Samuel Ortom na Benue da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu ta koma ‘Integriy Group’ a yanzu.
Baya ga gwamnonin, kungiyar na dauke da manyan masu fada aji a PDP wadanda suka nace sai dai Ayu ya sauka kan hujjar cewa babu yadda za a yi shugaban jam’iyya da dan takarar shugaban kasa su fito daga yanki guda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
G5 ta samu karuwa ta koma G6, Umahi
Da yake jawabi ga Wike a ranar Talata yayin kaddamar da wata hanya a Ribas, Umahi ya yi misali da sukar da shi da sauran gwamnonin da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC suka sha.
Sai dai kuma, ya ce ya goyi bayan matsayin gwamnonin G5 sannan ya ayyana kansa a matsayin mamba a kungiyar.
Gwamnan na Ebonyi ya ce:
“Dole kasarmu ta ga hikima a abun da muke yi. Yakinka ba na son rai bane; kana yaki ne don hada kan kasar nan. Kuma Allah na tare da kai. Ina mai baka tabbacin cewa ina tare da kai, ina goyon baya da gabanka, muna tare da kai kuma mun yi hadaka a wannan.
“Amma a yau, ka san cewa gwamnonin nan da ka so tsigewa ko kake kan hanyar tsigewa kafin ka watsar, mun kafa G4 – sune gwamna Wike, ni, Cross River da Zamfara. Akwai wasu G4 din.
“Saboda haka an bunkasa G5 zuwa G6. Nima na zama mamban G6 yanzu. Kuma ya mai girma gwamna, bari na sanar da aki wani abu, zan yi fafutukar Ciyaman da kai. Amma kujerar mataimaki, babu wanda zai karbe shi daga hannuna.
“Saboda haka, wannan kungiya ta ‘Integrity Group’ idan ka kira taro, dole ka kira ni. Gwamnoni da dama na so su shigo cikin wannan tafiyar; saboda sun ga cewa akwai ceto ga kasarmu a abun da kake yi. Saboda haka, ina so na jinjina maka.”
Wike ya fasa kwai, ya fadi cin fuskar da Atiku ya yiwa Jonathan a 2015
A wani labarin, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya zargi Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP da muzanta Gooluck Jonathan lokacin da tsohon shugaban kasar ya hadu da shi don neman goyon bayansa a 2015.
Wike ya ce sharadin da Atiku ya bayar shine cewa Jonathan ya hakura da tikitinsa duk da cewar ya bisa har Landan don neman yardarsa.
Asali: Legit.ng