Rikicin PDP: Gwamnonin G5 da Wasu Manyan Jiga-Jigan Jam’iyyar Na Ganawa a Legas

Rikicin PDP: Gwamnonin G5 da Wasu Manyan Jiga-Jigan Jam’iyyar Na Ganawa a Legas

  • Gwamnonin PDP biyar sun zauna da wasu manyan jiga-jigai da fusatattun 'ya'yan jam’iyyar a jihar Legas
  • Ana tsammanin bayan sun tattauna ci gaban da ke jam'iyyar a yanzu, gwamnonin na G5 zasu san matakin dauka na gaba
  • Babbar jam'iyyar adawar kasar dai na fama da rikici wanda yaki ci yaki cinyewa gabannin babban zaben 2023

Lagos - Gwamnonin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) da wasu fusatattun ‘ya’yan jam’iyyar suna cikin wata ganawa mai muhimmanci wanda ke gudana yanzu haka a jihar Lagas.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ganawar tasu ba zai rasa nasaba da fafutukar neman a tsige shugaban babbar jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu daga kan kujerarsa ba.

Gwamnonin PDP
Rikicin PDP: Gwamnonin G5 da Wasu Manyan Jiga-Jigan Jam’iyyar Na Ganawa a Legas Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Wata majiya da ke da masaniya kan taron, ta ce taron zai ba Wike da hadimansa damar sake bitar ci gaban da aka samu na baya-bayan nan a jam’iyyar kafin su dauki mataki na gaba.

Kara karanta wannan

Mai Bakin Cin Rashawa Bai Isa ya Jagoranci Kamfen ba, Wike ga Shugaban PDP

Kamar yadda jaridar New Telegraph ta rahoto, ana sa ran Gwamna Wike da mukararrabansa za su yi jawabi ga manema labarai bayan taron.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Manyan jiga-jigan PDP da suka halarci taron na Legas

Gwamnonin G5 da ake sa ran zasu halarci taron sun hada Nyesom Wike na jihar Ribas, Samuel Ortom na jihar Benue, Seyi Makinde na jihar Oyo, Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu da kuma Okezie Ikpeazu na jihar Abia.

Sauran mahalarta taron sune tsohon gwamnan jihar Ondo, Dr Olusegun Mimiko, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayo Fayose, tsohon gwamnan jihar Cross River, Mista Donald Duke.

Sai tsohon gwamnan jihar Plateau, Mista Jonah Jang da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Cif Bode Gorge, tsohon Atoni Janar kuma minsitan shari'a, Mista Bello Adoke.

Hakazalika, mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Mista Taoferk Arapaja, Sanata Nasif Suleiman, Mista Nnena Ukeje, Sanata S. O. Onor ada Sanata Mao Ohabunwa duk sun hallara.

Kara karanta wannan

Wike Ya Sake Tada Kura, Ya Ce PDP Za Ta Gane 'Khaki Ba Leda Bane'

A shirye muke muyi sulhu da Atiku, Wike

Ku tuna cewa alaka ta yi tsami tsakanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da Gwamna Wike.

Rikicin nasu ya samo asali ne tun bayan kammala zaben fidda dan takarar jam’iyyar inda gwamnan na jihar Ribas yace lallai sai dai a tsige Ayu daga shugabancin jam’iyyar sannan a baiwa yankin kudu damar samar da wanda zai maye gurbinsa.

Sai dai kuma Wike ya ce su a shirye suke suyi sulhu da Atiku amma sai dai idan sun yi abun da yakamata da adalci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel