Sabon Hasashe Ya Nuna Yadda Takarar 2023 Za Ta Kare Tsakanin APC, PDP, NNPP da LP
- Kamfanin Nextier ya yi hasashe a kan yadda mutane za su zabi ‘yan takaran shugaban kasa a 2023
- Mafi yawan mutanen da aka zauna da su sun ce Peter Obi na jam’iyyar adawa ta LP za su zaba a badi
- An cire Jihohin Legas, Adamawa, Anambra da Kano – inda ‘yan takaran suka fito, a wajen binciken
Abuja - Idan hasashen da kamfanin Nextier suka shirya ya tabbata gaskiya, Peter Obi ne zai zama sabon shugaban kasar Najeriya a Mayun shekarar 2023.
Hasashen Nextier ya nuna jam’iyyar LP za tayi galaba a zaben shugaban kasa da za ayi a Najeriya. Premium Times ta fitar da wannan rahoto a ranar Litinin.
An gudanar da wannan bincike ne ta hanyar tattaunawa da mutum 2, 000 da za suyi zaben shugaban kasa daga jihohi 12 da ake da su a shiyyoyin kasar nan.
Nextier sun ce ba suyi amfani da jihohin da ‘yan takaran suka fito a wajen binciken na su ba. A karshe aka fahimci APC, PDP da kuma LP ne suke kan gaba.
Ba a maganar NNPP a 2023?
Abin da binciken ya nuna shi ne ‘dan takaran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ba zai zo a sahun farko ba, duk da yana da goyon baya a Arewa maso yamma.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Rahoton da The Guardian ta fitar a makon nan ya nuna Obi yana da rinjayen goyon baya a kauyuka da kuri’u 40.37%, PDP da APC na biye da 26.7% da 20.47%.
A karshe 30% sun nuna LP za su zaba a 2023, Atiku Abubakar ya samu 17.3%, shi kuma Bola Tinubu yana da 4.98% sai Rabiu Kwankwaso ya kare da -8.70%.
Atiku Abubakar da Tinubu sun fi farin jini a wajen mutanen da ba suyi karatun boko ba. Mafi yawan musulman da aka yi magana da su sun ce za su zabi PDP.
Yadda za ayi zabe a kowace shiyya
Kamfanin yace hasashensa ya nuna masa kusan 60% na mutanen Benuwai da Nasarawa a Arewa maso tsakiya za su zabi LP, PDP da APC za su raba 35%.
A Arewa maso gabas, Atiku yake gaba da 50.3% sai jam’iyyar APC mai-mulki a baya da 27.2%, NNPP ta tashi da 14.6% na kuri’un yayin da Obi ya samu 5.8% rak.
A jihohin Kudu maso Kudu, LP ta samu 67% na kuri’in da aka kada, PDP da APC sun samu 11% da 10.7%. A yankin Kudu maso gabas kuwa LP tana da har 94%.
A shiyyar Kudu maso yamma, 37.4% sun karkata ga Tinubu, Obi ya samu 24%, Atiku yana da 16.5%, sai Sanata Kwankwaso da NNPP suka tsira da 2.3% kacal.
Hadin-gwiwar LP/NNPP
An samu rahoto da Rabiu Musa Kwankwaso ya yi bayanin zaman da aka yi tsakanin bangaren jam’iyyar NNPP da LP da inda aka ci karo da tasgaro a tattaunawar.
Jam’iyyun biyu sun yi niyyar dunkulewa ta yadda Kwankwaso zai hada-kai da Peter Obi saboda a lashe zabe amma dai hakan ya faskara saboda rashin jituwa.
Asali: Legit.ng