Wasu Magoya-bayan Jonathan Sun Jingine Atiku da PDP, Sun Tsaida ‘Dan takara Dabam
- ‘Yan kungiyar Citizens Network For Peace and Development in Nigeria za su bi Jam’iyyar APC 2023
- Sakataren Kungiyar CNPDN yace suna goyon bayan Bola Tinubu ne domin ganin mulki ya koma Kudu
- Francis Okereke Wainwei yana ganin Tinubu ya fi kowa cancanta a ‘yan takaran da suka fito daga Kudu
Wata kungiya mai suna Citizens Network For Peace and Development in Nigeria (CNPDN) tace tana goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu a zaben 2023.
The Cable tace ‘yan kungiyar CNPDN ne suka sayawa Dr. Goodluck Jonathan fam din neman takarar shugaban kasan 2023 a karkashin jam’iyyar APC.
Babban Sakataren CNPDN na kasa, Francis Okereke Wainwei ya yi jawabi a ranar Asabar, yace dole ne mulki ya koma hannun ‘yan kudancin Najeriya.
Francis Wainwei a madadin kungiyar yace tun da dai Goodluck Jonathan bai cikin masu takarar shugabancin kasar nan, za su goyi-bayan Bola Tinubu.
Meyasa sai Tinubu?
Sakataren yake cewa a duk masu neman mulkin Najeriya daga yankin Kudu, babu wanda yake da mutane, kuma zai iya cin zabe irin ‘dan takaran na APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
The Nation tace Wainwei wanda mutumin jihar Bayelsa ne, ya shaidawa manema labarai cewa kishin kasa ba zai kyale su su ki shiga harkar siyasa ba.
Mista Wainwei yace ‘yan kungiyar CNPDN za suyi bakin kokarinsu wajen ganin sun taka rawar gani zaben wanda zai gaji Muhammadu Buhari a Mayun badi.
“Mun dauki lamarin da matukar muhimmanci domin Najeriya tana bukatar mai hangen nesa, wanda ya cancanta, mara kabilaci da zai iya hada-kan jama’a.
Mun duba kwarewa, sanin siyasa da karbuwar ‘yan takaran Kudancin Najeriya, sai muka gane Asiwaju Bola Ahmed na APC ya sha gaban sauran ‘yan takara.
Saboda haka muna masu cikakken nuna goyon bayanmu ga ‘dan takaran APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda muke marawa baya a 2023.”
- Francis Okereke Wainwei
Ministan harkar gona, Dr. Mohammad Abubakar da tsohon shugaban RMFAC, Elias Mbam da kungiyoyi da-dama sun nuna goyon bayansu ga APC a taron.
Rabiu Musa Kwankwaso da Afenifere
Rahoto yace Rabiu Musa Kwankwaso ya je yawon siyasa a Legas, kuma ya yi nasarar kara raba kan Kungiyar nan mai kare hakkin Yarbawa watau Afenifere.
A halin yanzu kungiyar Afenifere ta nuna tana goyon bayan Peter Obi na LP, Bola Tinubu na APC da kuma shi Rabiu Kwankwso da ke yin takara a NNPP
Asali: Legit.ng