Wata Sabuwa, Makusantan Jonathan Sun Ayyana Goyon Baya Ga Tinubu a 2023

Wata Sabuwa, Makusantan Jonathan Sun Ayyana Goyon Baya Ga Tinubu a 2023

  • Ƙungiyar magoya bayan tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ta yanke hukunci kan wanda zai gaji Buhari
  • CNPDN wacce ta matsa wa Jonathan ya sake shiga tseren takara, ta jaddada cewa ya zama tilas mulkin Najeriya ya koma kudu
  • Bayan nazari da shawarin masu ruwa da tsaki a cewar Sakataren ƙungiyar, sun ɗauki Bola Tinubu na jam'iyyar APC

Abuja - Manyan jiga-jigan 'yan amutun tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da makusantansa sun ayyana cikakken goyon bayansu ga ɗan takarar APC, Bola Tinubu.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa magoya bayan ƙarƙashin kungiyar Citizens Network For Peace and Development in Nigeria (CNPDN) sun bayyana matsayarsu ne yayin zantawa da manema labarai a Abuja.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Wata Sabuwa, Makusantan Jonathan Sun Ayyana Goyon Baya Ga Tinubu a 2023 Hoto: thecalbe.ng
Asali: UGC

Sun ce tun da ubangidansu Goodluck Jonathan bai shiga takarar shugaban ƙasa a 2023 ba, abu na gaba da ya dace su sa a gaba shi ne goyon bayan Bola Tinubu na jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Atiku Ko Tinubu? Daga Karshe, Tsohon Gwamna Na Hannun Daman Wike Ya Faɗi Wanda Zai Goyi Baya a 2023

A cewarsu, tsohon gwamnan Legas, Tinubu, ne kaɗai daga cikin 'yan takara 18 ke da tsari da kwarewar lashe babban zaɓe mai zuwa koda kuwa an jingine batun cewa ɗan kudu ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

CNPDN na cikin sahun gaba a cikin ƙungiyoyin da suka nemi tsohon shugaba Jonathan ya nemi takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar APC.

Gamayyar kungiyar ta jawo manyan shugabanni a kudancin Najeriya domin su sa baki Jonathan ya amince da bukatar sake neman kujera lamba ɗaya a Najeriya.

Sakataren CNPDN na ƙasa, Mr. Francis Okereke Wainwei, ɗan asalin jihar Bayelsa, ya shaida wa yan jarida a Abuja cewa a matsayinsu na masu kishin ƙasa ba zasu tsame hannu su ƙi sa baki a zaɓe mai zuwa ba.

The Cable ta rahoton Sakataren na cewa:

"Bayan dogon nazari da shawarin manyan masu ruwa da tsaki na kowace shiyyar ƙasar nan, mun ƙarƙare cewa gogagge kuma kwararren ɗan takarar shugaban ƙasa daga kudu ya dace da Najeriya a 2023."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Sifetan Yan Sanda Na Ƙasa Ya Gana da Jiga-Jigan Siyasa 18 a Abuja

"Bugu da ƙari mun sanya yan takarar kudu a Silelin gogewa, sanin siyasa da karɓuwa a matsakin ƙasa, kuma mun gano cewa Bola Tinubu, mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar APC ya kere saura."
"Sakamkon haka muke ayyana cikakken goyon bayanmu ga Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin wanda muka zaɓa ya zama shugaban kasa na gaba a zaɓe mai zuwa."

Sakataren ya ƙara da cewa zargin takardun bogi da hannu a safarar miyagun kwayoyi da ake wa Tinubu, tun da daɗe wa aka rufe wannan shafin.

Adalci Shi ne ɗan kudu ya karbi mulki bayan Buhari - Ortom

A wani labarin kuma gwamna Samuel Ortom yace idan har adalci za'a bi, bayan shekaru 8 ɗin Buhari, Ɗan kusu ya dace da Najeriya

Da yake jawabi a wurin kaddamar da fara yakin neman zaɓen PDP a jihar Ribas, Gwamnan Benuwai yace gwamna Wike ya haɗa dukkanin abinda ake bukata na jan ragamar Najeriya

Kara karanta wannan

Kamfen Jos: Dalilin da Ya Sa Zan Taimakawa Tinubu Ya Gaji Kujerata a 2023, Shugaba Buhari

Sai dai a cewarsa, wasu makiyan ci gaba masu hana ruwa gudu ne suka yi kutun-kutun aka kayar da Wike a zaɓen fidda gwanin PDP a watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel