Bayan Ganawa Da Babban Na Hannun Damar Atiku, Wike Ya bayyana Matsayinsa na Karshe Kan Rikicin PDP

Bayan Ganawa Da Babban Na Hannun Damar Atiku, Wike Ya bayyana Matsayinsa na Karshe Kan Rikicin PDP

  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da mukarrabansa sun ziyarci jihar Bauchi a ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamba
  • Da yake magana kan rikicin cikin gida da ya dabaibaye PDP, Wike ya bayyana cewa har yanzu kofar sulhu tsakaninsu da shugabancin jam'iyyar a bude take
  • Gwamnan na jihar Ribas ya jadadda cewar abun da suke bukata daga shugabancin jam’iyyar kawai shine yin abun da ya dace gabannin zaben 2023

Gwamna Nyesome Wike na jihar Ribas ya ce shi da mukarrabansa a shirye suke suyi sulhu da shugabancin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Channels TV ta rahoto.

Takaddama ta shiga tsakanin wasu gwamnonin PDP biyar da jam'iyyar bayan gwamnan na jihar Ribas ya sha kashi a hannun Atiku Abubakar a zaben fidda dan takarar shugaban kasa.

Gwamnonin PDP
Bayan Ganawa Da Babban Na Hannun Damar Atiku, Wike Ya bayyana Matsayinsa na Karshe Kan Rikicin PDP Hoto: Rivers Mirror
Asali: Facebook

Bayan zaben, gwamnonin biyar sun bukaci Iyorchia Ayu ya yi murabus daga matsayin shugaban PDP na kasa don baiwa wani da ba dan arewa ba damar darewa kujerar.

Kara karanta wannan

2023: Wasu Daga Cikin Gwamnonin Tsagin Wike Na Shirin Yaudararsa, Zasu Koma Bayan Atiku

Har ila yau, gwamnonin sun fita daga kwamitin yakin neman zaben Atiku sannan duk wani yunkuri na sulhu ya ci tura.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnonin G5 sune bangon jinginar PDP

Wike ya nuna karfin gwiwa cewa idan tsagin Atiku da shugabancin jam'iyyar suka ki yarda ayi sulhu toh PDP zata sha kaye a zaben shugaban kasa na 2023, jaridar The Sun ta rahoto.

Sai dai kuma, da yake jawabi bayan takwarorinsa hudu da ake kira da G5 sun ziyarci gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, Wike ya bayyana cewa basu rufe kofar sulhu ba.

"Na sha fadi sau da dama cewa muna nan don sulhu. Bamu taba kulle kofar sulhu ba. Abun da muke nema kawai shine daidaito, adalci da gaskiya. Bamu taba rufe kofa ba kuma ba za mu taba rufe kofa ba.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar PDP Ta Fadi Wanda Atiku Zai Mika Wa Mulki Bayan Gama Wa'adinsa

"Abun da kawai muke cewa shine, duba, mu yi abun da yakamata ayi. Idan aka yi abun da yakamata, kasar gaba daya zata san cewa an gama zabe. Wadannan G5 da kuke gani sune ginshikin jam'iyyar don haka ba zamu rufe kofar sulhu ba; a shirye muke ayi sulhu kodayaushe, a kowani lokaci."

Gwamnonin sun kai ziyara jihar Bauchi ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewa Gwamna Bala Mohammed na shirin ficewa daga kwamitin yakin neman zaben shugabancin jam'iyyar kan ikirarin cewa masu biyayya ga Atiku na aiki don hana shi zarcewa.

Gwamna Mohammed ya ziyarci Atiku a ranar Talata a Abuja duk a kokarin magance matsalar da ta dabaibaye babbar jam'iyyar adawar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel