Sani: Gwamnatin Buhari Ta Ce Za Ta Tsamo Mutum Miliyan 100 Daga Talauci Amma Ta Jefa Miliyan 133 Cikin Talauci

Sani: Gwamnatin Buhari Ta Ce Za Ta Tsamo Mutum Miliyan 100 Daga Talauci Amma Ta Jefa Miliyan 133 Cikin Talauci

  • Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a jihar Kaduna ya yi wa gwamnatin Buhari izgili kan jefa yan Najeriya cikin talauci
  • Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta hannun Ma'aikatar Kwadago da samar da ayyuka ta yi alkawarin tsamo yan Najeriya miliyan 100 daga talauci
  • Sai dai a ranar Alhamis, hukumar kididdiga ta kasa NBS ta fitar da alkalluma da suka ce yan Najeriya miliyan 133 sun fada matsananciyar talauci

Twitter - Sanata Shehu Sani ya yi wa gwamnati mai ci yanzu izgili saboda gazawarta na tsamo yan Najeriya miliyan dari daga talauci a maimakon hakan ta jefa mutane miliyan 133 cikin mummunan talauci.

Tsohon sanatan na Kaduna ta tsakiya ya bayana hakan ne cikin wani rubutu da ya saki a sahihin shafinsa na Tuwita a ranar Juma'a 18 ga watan Nuwamban shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Majalissar Dattijai Omo Ovie-Agege Yace Shine Ya Dakatar da Kudirin Tsige Shugaba Buhari

Shehu Sani
Shehu Sani: A Maimakon Tsamo Mutum Miliyan 100 Daga Talauci, Buhari Ya Jefa Mutane Miliyan 133 Cikin Talauci. Hoto: @daily_trust.
Asali: Facebook

Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin gwamnati na tsamo yan Najeriya guda miliyan 100 daga talauci zuwa 2030.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakatariyar dindindin na Ma'aikatar Kwadago Da Samar Da Ayyuka, Ms Kachollum Daju, ta fada wa manema labarai a Satumba cewa shirin na gwamnati na samo mutane daga talauci zai yiwu, idan masu ruwa da tsaki suka taka rawar da ake tsammani yadda ya dace.

Yan Najeriya miliyan 133 na zama cikin matsanancin talauci - rahoton NBS na 2022

Amma, Hukumar kididdiga ta kasa, NBS, a ranar Alhamis ta sanar da cewa adadin yan Najeriya da ke zama cikin matsanancin talauci ya haura miliyan 133, kimanin kashi 63 cikin 100 na kasar.

A martaninsa kan lamarin, Sani, a shafinsa na Twitter ya ce a hukumance gwamnatin ta jefa mutane miliyan 133 cikin talauci.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Amince da Tsige Shugaban NYSC Nan Take Kan Wani Muhimmin Abu

Kalamansa:

"Sun yi alkawarin tsamo mutane miliyan dari daga talauci; yanzu a hukumance sun jefa mutane miliyan dari da talatin da uku cikin zuzurfan talauci."

Yan Najeriya Miliyan 133 Ne ke Rayuwa Cikin Matsanancin Talauci, Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa kashi 63 cikin dari na mutanen da ke rayuwa a kasar wanda yayi daidai da mutum miliyan 133 suna rayuwa ne cikin matsanancin talauci.

An gabatar da wannan kiyasin ne a yayin kaddamar da binciken Nigeria’s Multidimensional Poverty Index a Abuja a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164