Shugaba Buhari Ya Gaggauta Tunbuke Darakta Janar Na NYSC Kan Wani Abu Da Ya Taso

Shugaba Buhari Ya Gaggauta Tunbuke Darakta Janar Na NYSC Kan Wani Abu Da Ya Taso

  • An tsige Birgediya Janar Mohammed Fadah daga kujerar shugabancin hukumar yiwa kasa hidima wato NYSC
  • Fadah wanda ya zama Darakta Janar na NYSC a watan Mayun 2022 ya karbi aiki ne daga hannun Manjo Janar Shuaibu Ibrahim
  • Mai magana da yawun hukumar ta NYSC, Eddy Megwa, ya tabbatar da lamarin sai dai bai yi karin haske kan dalilin sauke shi ba

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da gaggauta tsige Mohammed Fadah a matsayin darakta janar na Hukumar kula da dalibai da ke yi wa kasa hidima wato NYSC, jaridar TheCable ta rahoto.

Majiyoyi sun bayyana cewa shugaban kasar ya dauki wannan matakin ne a ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamba, kuma hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake nuna damuwa kan rashin kwarewarsa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Nada Sabuwar Mukaddashin Daraktan NAFDAC

Mohammed Fadah
Shugaba Buhari Ya Gaggauta Tunbuke Darakta Janar Na NYSC Kan Wani Abu Da Ya Taso Hoto: Thecable
Asali: UGC

An tsige Fadah ne yan watanni bayan ya karbi shugabancin hukumar, domin ya kama aiki ne a watan Mayun 2022 kuma shine mutum na 19 da ya riki mukamin darakta janar na NYSC.

Daraktan labarai kuma jami’in hulda da jama’a na hukumar NYSC, Eddy Megwa, ya tabbatar da lamarin ga jaridar Leadership amma bai bayyana dalilin sauke shi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin tanadin da ya yiwa hukumar NYSC a lokacin da aka nada shi harda inganta tsaro da jin dadin masu yiwa kasa hidima, inganta jindadin ma’aikata da kuma habbaka ci gaban ayyukan NYSC.

Fadah zai mika ragamar shugabanci ga babban jami'i a hukumar don rikon kwarya

A halin da ake ciki, bayan tsige shi da aka yi, an bukaci Fadah ya mika ragamar shugabanci ga babban jami’i na gaba a cikin hukumar ta NYSC.

Kara karanta wannan

Sauya Fasalin Naira: Miyetti Allah Ta Roki CBN Ya Kara Wa'adi Saboda Kada Fulani Suyi Hasara

Ana sa ran duk wanda zai karbi jagoranci daga hannun Fadah zai yi aiki a matsayin mukaddashin darakta janar na hukumar bautar kasar har zuwa lokacin da za a sanar da sabon nadi.

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta jaddada matsayinta na cewar ba za ta biya malaman kungiyar ASUU albashin aikin da basu yi a lokacin da suka tafi yajin aiki.

Kamar yadda ministan ilimi, Malam Adamu Adamu ya bayyana, gwamnatin Muhammadu Buhari ta ce tana nan a kan bakarta na 'babu aiki babu biya' bayan ta biya malaman jami'ar rabin albashi a watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel