Ana Tsaka da Rikici da Atiku, Wike Zai ba Peter Obi Gudumuwar Lashe Zabe a 2023
- Gwamnan jihar Ribas ya yabi Peter Obi yayin da ya kaddamar masa da gadar da ya gina a Oroworokwo
- Mai girma Nyesom Wike ya dade yana rigima da Atiku Abubakar mai neman mulkin Najeriya a PDP
- Wike ya gayyaci Obi zuwa jiharsa, har kuma ya nuna zai taimaka masa duk bambancin jam’iyyarsu
Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi alkawarin taimakawa Peter Obi mai neman zama shugaban kasa a karkashin jam’iyyar LP.
Daily Trust a wani rahoto da ta fitar a ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwama 2022, tace Gwamnan Ribas ya yi alkawarin ba Peter Obi gudumuwa.
A duk lokacin da ‘dan takaran na LP ya zo jihar Ribas domin ya yi kamfe, Wike yace zai taimaka masa da abubuwan da yake bukata na kai-komo.
Wike yace tsohon gwamnan na Anambra yana da duk abin da ake bukata domin ya rike Najeriya.
Ka rabu da batun Gwamna a LP
Duk da ya sha alwashin taimakawa Obi a zaben shugaban kasa, Gwamnan ya fadawa ‘dan takaran ya hakura da maganar cin zaben Gwamna a Ribas.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An rahoto Gwamna Wike yana fadawa Obi cewa ka da ya yi asarar kudinsa domin a Ribas, jam’iyyar LP ba ta da ‘dan takaran Gwamna a zaben badi.
"Duk lokacin da za kayi kamfe a jihar nan, ka sanar da ni. Za a ba ka duk wata gudumuwar kai-komo da ake bukata.
Amma ka da ka bata lokacinka a kan kowa a zaben ‘dan takaran gwamna saboda LP ba ta ‘dan takara a jihar Ribas."
- Nyesom Wike
Mai girma gwamnan ya yi watsi da Atiku Abubakar da sauran jiga-jigan jam’iyyar PDP, ya gayyaci Obi ya kaddamar da wata gadar sama da ya gina.
Obi ya ziyarci jihar Kudu maso kudancin kasar ne domin kadamar da gadar Oroworokwo.
Punch tace wadanda suka yi wa ‘dan takaran raiya sun hada da Dr. Yusuf Datti Baba-Ahmed mai neman zama mataimakin shugaban kasa a LP.
Rikici a Katsina
An ji labari rigimar cikin gida ya jawo abubuwa sun jagwalgwalewa PDP a Katsina. An shiga rudani bayan samun shugabanni biyu a wata daya.
Wani Jami’in APC na reshen jihar Katsina, Mustapha Shittu Mahuta yace sun yi karar uwar jam’iyya a kotu saboda canza shugaban reshensu.
Asali: Legit.ng