Rikicin PDP ya Rincabe, Shugaban Jam’iyya da aka Tsige a Katsina Ya Dumfari Kotu

Rikicin PDP ya Rincabe, Shugaban Jam’iyya da aka Tsige a Katsina Ya Dumfari Kotu

  • Rigimar cikin gida ya kaure a jam’iyyar hamayya ta PDP a dalilin shugabanci na reshen Katsina
  • Mutanen Lawal Uli sun kai kara domin kotu ta sauke shugaban jam’iyyan jihar Katsina da aka nada
  • Mustapha Shittu Mahuta yace doka ba ta goyon bayan matakin da Shugabannin PDP suka dauka

Katsina - Rikicin da jam’iyyar PDP take fama da shi a reshen jihar Katsina ya canza salo bayan da aka ji ‘yan bangaren Lawal Uli sun shigar da kara a kotu.

Daily Trust ta rahoto cewa Lawal Uli ya shigar da kara a gaban Alkali, yana neman kotu ta hana Lawal Magaji darewa kan kujerar shugaban jam’iyyar PDP.

Mai ba jam’iyyar PDP ta reshen jihar Katsina shawara a kan harkar shari’a, Barista Mustapha Shittu Mahuta ya shaidawa manema labarai sun kai kara.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Sifetan Yan Sanda Na Ƙasa Ya Gana da Jiga-Jigan Siyasa 18 a Abuja

Mustapha Shittu Mahuta yake cewa sun bukaci Alkali ya umarci Lawal Magaji ya daina bayyana kansa a matsayin wanda yake rike da jagorancin jam’iyya.

Ana shari'a a kotu - Mahuta

“Mun je kotu domin neman taka burki. Mun shigar da kara muna neman ‘dan bangaren Lado ya daina bayyana kan shi a matsayin shugaban jam’iyya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma kotu ta umarci a tsaida maganar, kuma hakan muka yi. Kotu tace tana bukatar sauraron bangarori biyu, an daga karar zuwa 29 ga Nuwamba."

- Mustapha Shittu Mahuta

'Yan PDP
Taron PDP a Katsina Hoto: www.nairaland.com
Asali: UGC

Sai abin da doka tace

Barista Mahuta ya kafa hujja da sashe na 47(6) na kundin tsarin mulkin PDP, yace babu dalilin nada sabon shugaba a dalilin takarar Salisu Yusuf Majigiri.

Hon. Salisu Majigiri yana neman takarar ‘dan majalisar wakilan tarayya a 2023, Mahuta yace wannan ba dalili ne na nada sabon shugaban jam’iyya ba.

Kara karanta wannan

Kotu ta bar ‘Yan Jam’iyyar APC Cikin Rikici Bayan Soke Zaben ‘Dan Takaran Gwamna

‘Dan siyasar yana neman kujerar ‘dan majalisar Mashi/Dutsi, ganin cewa bai shiga ofis ba tukuna, Barista Mahuta yace doka ba ta hana shi rike jam’iyya ba.

Lauyan yace a dalilin haka aka nada Hon. Lawal Uli ya zama shugaban rikon kwarya, kafin a je ko ina kuma sai ga shi PDP NWC ta sake nada wani dabam.

Jaridar ta rahoto jami’in yana cewa zaben shugabannin ake yi, a maimakon uwar jam’iyya ta nada su, kuma shugabannin mazaba ke cike gurbin da aka samu.

Atiku v G5

A halin yanzu, kun samu rahoto da ya nuna wasu Gwamnoni ba za su bi tafiyar Atiku Abubakar ba saboda sabanin da aka samu tsakaninsu da ‘dan takaran na su.

Gwamnonin jihohi biyu daga yankin Arewa da wasu biyun daga Kudancin Najeriya sun turje wajen taimakawa PDP a zaben shugaban kasa da za a shirya a badi.

Kara karanta wannan

Yadda ‘Dan Majalisar Legas Ya Rasu Wajen Taron Kamfen Bola Tinubu a Garin Jos

Asali: Legit.ng

Online view pixel