Kotu ta bar ‘Yan Jam’iyyar APC Cikin Rikici Bayan Soke Zaben ‘Dan Takaran Gwamna

Kotu ta bar ‘Yan Jam’iyyar APC Cikin Rikici Bayan Soke Zaben ‘Dan Takaran Gwamna

  • Kotun tarayya ta karbe takarar Gwamna da Jam’iyyar APC ta ba Akanimo Udofia a Jihar Akwa Ibom
  • Kamar yadda Ita Enang ya shigar da kara, an gamsu Udofia yana PDP ya shiga zaben yin takara a APC
  • Shugaban APC na Akwa Ibom, Tunde Ajibulu ya soki hukuncin Alkalin, yace Udofia ‘dan jam’iyya ne

Akwa Ibom - Ita Enang mai neman takarar Gwamna a APC da Tunde Ajibulu wanda shi ne shugaban jam’iyya a jihar Akwa Ibom sun samu sabani.

Rahoton Premium Times ya nuna bambancin da ya shiga tsakanin ‘yan siyasar ya bayyana a fili bayan ruguza takarar Akanimo Udofia da kotu tayi.

Alkali Agatha Okeke ta babbar kotun tarayya a garin Uyo, ta zartar da hukunci cewa APC ta sake shirya zaben tsaida gwanin gwamna a Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Sanata Binani vs Nuhu Ribadu : Kotu Daukaka Ta shirya yanke hukunci kan zaben fidda gwanin jihar Adamawa

Udofia bai yi kwana 30 a APC ba?

Jaridar tace Ita Enang ya shigar da kara, ya nemi a karbe takara daga hannun Akanimo Udofia bisa zargin shi ba ‘dan APC ba ne da ya tsaya zabe.

Mai shari’a Agatha Okeke ta gamsu da wannan, ta ruguza zaben da ya kawo Udofia, ta kuma haramtawa ‘dan siyasar shiga sabon zaben da za a shirya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da suka bayyana a gidan talabijin Channels a ranar Talata, Tunde Ajibulu ya nuna mamakinsa a kan hukuncin da Alkalin babban kotun ta zartar.

'Yan APC
APC a Akwa Ibom Hoto: freedomonline.com.ng
Asali: UGC

Hukuncin ya daure kan APC

Ajibulu yace ya gagara gane abin da ya sa kotu tace Udofia ba ‘dan PDP ba ne, alhali jam’iyya ta tabbatar da cewa yana cikin ‘ya ‘yanta kafin zaben.

“Idan APC tace Akanimo Udofia ‘dan jam’iyya ne, ya shiga zaben gwani, kuma an aikawa INEC sunanta, hakan na nufin ya samu takara kenan.

Kara karanta wannan

Kotu ta Hana APC Sakat, An Sake Ruguza Zaben Tsaida Gwanin da Aka Yi a Taraba

Na rasa yadda Alkali za ta zo tace Akanimo Udofia bai cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC.”

- Tunde Ajibulu

Alkali tayi daidai inji 'Dan takara

Amma Sanata Ita Enang ya maidawa Ajibulu raddi a gidan talabijin, yace Udofia ya samu matsala tun daga sunayen da aka yi amfani da su wajen zabe.

Tsohon hadimin shugaban kasar yace APC ba ta san da zaman sunayen wadanda aka yi amfani da su wajen shirya zaben ‘dan takaran Gwamnan ba.

Haka zalika, Enang yace kotu tana da damar da za tace mutum bai cika sharadin zama ‘dan jam’iyya ba, nauyin haka bai rataya kan jam’iyya kadai ba.

Za a yaki Tinubu a N/Delta

Dazu an samu rahoto takarar Shugaban kasar Bola Tinubu da Jam’iyyar APC a Jihohin Kudu maso kudu watau Neja-Delta za ta gamu da barazana.

Kungiyar Alliance for Rescue of the Niger Delta Region, ARNDR ta nuna ba ta gamsu da rawar da Muhammadu Buhari ya taka a tsawon shekaru bakwai ba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotun Daukaka Kara ta Kori Akpabio Daga Takarar Sanata

Asali: Legit.ng

Online view pixel