Kishin-Kishin: Sanatoci 22, 'yan majalisun tarayya 50 na shirin komawa PDP kafin 2019
- Sanatoci 22, 'yan majalisun tarayya 50 na shirin komawa PDP kafin 2019
- PDP ta zayyana jahohi 15 da take sa ran kawowa jam'iyyar ta APC matsala a zaben mai zuwa
- PDP din na muradin kwato Bukola Saraki da kuma Yakubu Dogara
Kamar dai yadda muka samu daga majiyoyin mu, jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party (PDP) tuni ta fara zawarcin akalla yan majalisar dattijai 22 tare da 'yan majalisar wakilai 50 kafin zaben gama gari mai zuwa na 2019 daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.
KU KARANTA: An tura jiragen yaki 100 gano 'yan matan Dapchi
Haka zalika ma dai mun samu cewa jam'iyyar ta PDP ta zayyana jahohi 15 da take sa ran kawowa jam'iyyar ta APC matsala a zaben mai zuwa da suka hada da Kano, Kaduna, Osun, Imo, Kogi, Bauchi, Kwara da kuma Jigawa.
Sauran jahohin haka zalika sun hada da Benue, Plateau, Adamawa, Nasarawa, Zamfara, Sokoto sai kuma jihar Ekiti.
Haka nan kuma mun samu cewa manya manyan jam'iyyar ta APC da PDP din ke muradin kwatowa hadda shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki da kuma kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng