Oshiomhole Ya Dira Patakwal Yayin da Wike Ya Cigaba da Dasawa da Jiga-Jigan APC

Oshiomhole Ya Dira Patakwal Yayin da Wike Ya Cigaba da Dasawa da Jiga-Jigan APC

  • Awanni bayan halartar gangamin APC, Adams Oshiomhole ya tafi jihar Ribas domin amsa gayyatar gwamna Nyesom Wike
  • Tsohon shugaban APC na ƙasa ya isa gidan Wike da ke yankin ƙaramar hukumar Obio Akpor, zai kaddamar da wani aiki
  • Wike na cigaba da kulla alaƙar kawacce da kusoshin APC tun bayan ɓarkewar rigima tsakaninsa da shugabannin PDP

Rivers - Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya isa Patakwal domin kaddamar da sabuwar gadar, 'Rumueprikom Flyover' da gwamnatin Ribas ta gina karkashin mulkin gwamna Nyesom Wike.

Oshiomhole ya isa gidan kai-da-kai na gwamna Wike da ke ƙaramar hukumar Obio Akpor ta jihar Ribas awanni bayan halartar kaddamar da fara kamfen Bola Tinubu, mai neman shugaban kasa a APC a Jos.

Adams Oshiomhole da Wike a Patakwal.
Oshiomhole Ya Dira Patakwal Yayin da Wike Ya Cigaba da Dasawa da Jiga-Jigan APC Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Daily Trust tace Wike ya kara danƙon ƙawancensa da manyan jiga-jigan jam'iyya mai mulki tun bayan taƙaddamar da ta haɗa shi da shugabancin jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Hotuna: Jos Ta Cika Maƙil, Buhari da Gwamnoni Sun Dira Yayin da Tinubu Zai Bude Kamfen 2023

Gwamnan ya nemi tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP amma ya sha ƙasa a hannun tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan kuma Wike ya nuna sha'awar zama abokin takarar Atiku amma aka ɗauki takwaransa na jihar Delta, Ifeanyi Okowa, lamarin da ya ƙara harzuƙa shi.

Jim kaɗan bayan haka, Gwamna Wike ya fara kiraye-kirayen a sauya shugabancin babbar jam'iyyar adawa, inda yace ba zai yuwa ɗan takara da shugaban jam'iyya su hito daga yanki ɗaya ba.

Wike da wasu gwamnoni makusantansa sun sanar da janye wa daga kwamitin kamfen Atiku, suka kafa sharaɗin sauya Ayu a matsayin abu ɗaya da zai kawo zaman lafiya.

Duk da wutar rikici dake ƙara ruruwa a PDP, Wike ya gana da Bola Tinubu kana aka ga yana gayyatar ƙusoshin APC suna kaddamar da ayyukansa a Ribas.

Kara karanta wannan

Sabuwar Baraka: Sanatan PDP Ya Aje Atiku, Ya Yaba Wa Bola Tinubu Kan Wani Muhimmin Abu

Su wa Wike ya gayyata suka kaddamar da ayyuka?

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa daga cikin manyan jiga-jigan APC da suka kaddamar da ayyuka a Ribas akwai kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila.

Sai kuma gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da kuma Sanata Aliyu Wamakko, tsohon gwamnan jihar Sakkwato kuma jagoran APC a jihar, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Jam'iyyar PDP ta nuna rashin jin daɗinta kan halayyar Wike ta gayyato wasu bare a jam'iyyar suna buɗe ayyukansa amma gwamnan ya maida martanin cewa ba ya bukatar neman izini wajen yanke hukunci a jiharsa.

A wani labarin kuma Bola Tinubu ya sha alwashin tasa ƙeyar Peter Obi ya koma Anambra bayan ya lashe babban zaɓen 2023.

A jawabinsa na wurin kaddamar da yakin nan zaɓensa a Jos, Tinubu yace ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar LP, Peter Obi, ya gudu daga jiharsa ya koma zama a Legas.

Kara karanta wannan

Wani Gwamna Ya Jingine Tinubu, Atiku da Peter Obi, Ya Faɗi Wanda Yake Goyon Bayan Ya Gaji Buhari a 2023

Tsohon gwamnan ya yi ikirarin cewa Obi da magoya bayansa da ake kira Obidients ba su san hanyar da zata kaisu fadar shugaban kasa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel