Gwamna Ya Hana ‘Dan Takaran Shugaban Kasa Wurin Kamfe, Ya Kawo Dalilin Yin Haka

Gwamna Ya Hana ‘Dan Takaran Shugaban Kasa Wurin Kamfe, Ya Kawo Dalilin Yin Haka

  • Jam’iyyar LP ta bukaci tayi amfani da filin wasan Samuel Ogbemudia domin yin kamfe a jihar Edo
  • Gwamnati ba ta amince da wannan dama ba, sai dai Peter Obi ya yi taronsa a wajen filin na dabam
  • Gwamna Godwin Obaseki yace LP ta aiko masu da bukatarta a kurarren lokaci, shiyasa ba a dace ba

Edo - Gwamna Godwin Obaseki ya yi bayanin abin da ya hana jihar Edo bada damar ayi amfani da filin wasan Samuel Ogbemudia wajen kamfe.

The Cable tace Peter Obi neman zama shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar LP ya nemi a shi damar yin taro a filin wasan, amma aka hana shi.

Wannan mataki da gwamnatin jihar Edo ta dauka ya jawo magoya bayan Peter Obi sun yi ta suka, a karshe suka yi taron a wani filin taron kiristoci.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Jonathan da Tunzura Gwamnonin PDP 5 Su Juyawa Atiku Abubakar Baya

Amma da aka zanta da shi, Godwin Obaseki ya wanke gwamnatinsa daga zargi, ya bayyana abin da ya sa aka hana LP yin amfani da filin wasan.

An zanta da Gwamnan Edo

Mai girma Obaseki ya yi hira da gidan talabijin Channels TV a ranar Juma’a, 11 ga watan Nuwamba 2022, yace abin ya zo ne a kurarren lokaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Gwamnan, LP ta aiko da bukatar amfani da filin wasan ne a yammacin Laraba, hakan ya jawo rashin isasshen lokacin duba takardarta.

Peter Obi
Taron Peter Obi a Benin Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

An rahoto Obaseki yana mai cewa akwai tanadi na musamman da ake yi kafin a kai ga yin amfani da filin wasan wajen yin gangami ko taron siyasa.

Baya ga haka, Gwamnan yace akwai sauraran wuraren da za a iya amfani da wasu wajen kamfe.

Kwana daya suka ba mu - Obaseki

Kara karanta wannan

Tonon Sililin da Gwamnan Anambra Ya Yi Wa Peter Obi Ya Tsokano Masa Fushin 'Obidients'

“Na ji labari sun aiko da bukatarsu na amfani da filin wasan Samuel Ogbemudia ne a daren Alhamis.
Suna so suyi amfani da shi a safiyar Juma’a – Tazarar kwana daya kurum suka ba mu.
Ana aiki a kan wajen tsere. Sai an gyara wajen wasa domin a shiryawa taron. Ba haka kurum za a bada ba tare da an shirya ba.
Idan sun san za su yi gangami a Juma’a, me zai hana su ba mu lokaci mai yawa domin mu shirya, sai mu gindaya masu sharadi.”

Soludo ya fallasa Obi

Kuna da labari a lokacin da yana Gwamna a Anambra, Peter Obi ya dauki dukiyar Jiharsa ya juya a kamfanin giya, a karshe dai aka tafka asara.

Gwamna Charles Soludo ya bayyana cewa kudin Jihar Anambra da Obi ya sa a kamfanin giya ba su haifar da komai ba, da su da babu duk daya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Wani Babban Filin Wasanni a Najeriya Ya Ruguje, Mutane Sun Rasa Rayukansu

Asali: Legit.ng

Online view pixel