Wani Filin Wasanni a Najeriya Ya Rufta Kan Mutane, An Rasa Rayuka Da Dama

Wani Filin Wasanni a Najeriya Ya Rufta Kan Mutane, An Rasa Rayuka Da Dama

  • Rahoto daga Asaba, babban birnin jihar Delta ya nuna cewa babban filin wasanni na ƙasa da ƙasa Stephen Keshi ya samu matsala
  • Bayanai sun nuna cewa wani ɓangaren filin da ake aikin gina wa ya rufta kuma ya yi ajalin akalla rayukan mutane uku
  • Duk da babu wasu sahihan bayanai kan abinda ya haddasa lamarin amma ana ganin yana da alaƙa da saurin masu aikin na gama wa a lokaci

Delta - Wani sashi da ake aikin ginawa a babban Filinin wasanni na ƙasa da ƙasa, Stephen Keshi International Stadium dake Asaba, babban birnin jihar Delta, ya rufta kan mutane.

Jaridar Punch ta rahoto cewa rushewar ginin ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum uku a Filin wasannin yayin da wasu da dama suka jikkata aka gaggauta kai su Asibiti.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wasu Fitattun Malamai Biyu a Jihar Arewa

Stephen Keshi International Stadium.
Wani Filin Wasanni a Najeriya Ya Rufta Kan Mutane, An Rasa Rayuka Da Dama Hoto: punchng
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa ana aikin Ginin da yi wa Filin garambawul ne yayin da ake tunakarar bikin wasannin na ƙasa wanda aka shirya gudanarwa a Filin cikin wannan shekarar.

A baya-bayan nan ba da jimawa ba Ministan Matasa da wasanni, Sunday Dare, ya kai ziyarar duba yadda gyaran filin ke tafiya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Menene ya hadda rugujewar sashin Filin?

Duk da dai babu wani bayani a hukumance kan musabbabin rushewar Ginin amma ana ganin lamarin ba zai rasa nasaba da sauri-saurin da masu aikin ke yi na kammalawa a lokacin da aka ƙayyade musu ba.

Rushewar gini ba sabon abu bane a Najeriya, a wannan shekarar da muke ciki da 2021 da ta wuce faɗuwar gine-gine sun halaka mutane da dama.

Jihar Legas dake kudu maso yammacin Najeriya ce kan gaba wurin samun ibtila'in ruftawar gini, inda sai da ta kai ga gwamna Sanwo-Olu, ya dakatar da Daraktan hukumar kula da gine-gine (LASBCA).

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Tinubu Yayi Alkawarin Samar da Ayyuka 1m a Shekaru 2 na Farkon Mulkinsa

Mutum 14 Sun Kone Kurmus a Wani Mummunan Hatsari da Ya Auku a Kano

A wani labarin kuma wani mummunan Hatsarin mota tsakanin Motar Bus ta Kano Line da wata Jeep ya yi ajalin mutane 14 a Kano

Lamarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 7:30 na dare a kan babban Titin Gaya-Wudil ya jikkata wasu Fasinjoji shida suna kwance a Asibiti.

Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra (FRSC) na jihar Kano, Zubairu Mato, ya alaƙanta hatsarin da gudun wuce ƙima da kokawar tsere wa juna a babban Titi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel