IBB Zai Shiga Tsakani Don Sulhunta Atiku da Gwamnonin G-5 Masu Yiwa PDP Barazana

IBB Zai Shiga Tsakani Don Sulhunta Atiku da Gwamnonin G-5 Masu Yiwa PDP Barazana

  • Rahoto mai daukar hankali ya bayyana cewa, tsohon shugaban kasar Najeriya zai sulhunta Atiku da gwamnonin G-5
  • Gwamna Wike da wasu gwamnonin PDP hudu a kasar nan sun ce ba za su goyi bayan dan takarar shugaban kasansu ba
  • Tawagar G-5 ta kai ziyara jihar Bauchi, wasu rahotanni sun ce sun dura jihar ne a yunkurinsu na jawo gwamna Bala Muhammad cikinsu

Minna, jihar Neja - Akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa, tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya zai shiga tsakanin don warware rikicin cikin gida da PDP ke ciki.

Jaridar Leadership ta tattaro cewa, tsohon shugaban na Najeriya zai yi wata ganawa da dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da gwamoni biyar da ke adawa da ta tsarin shugabancin PDP da ake kira G-5 a birnin Minna ta Neja ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP Da Suka Bayar Da Sharudda A Bainar Jama'a Kafin Yi Wa Atiku Aiki A Jihohinsu

Wannan ganawa ta IBB da su Atiku za ta zo ne kwanaki uku bayan da ya zauna da dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.

Atiku zai shirya da su Wike, tsohon shugaban kasa ya sa baki
IBB Zai Shiga Tsakani Don Sulhunta Atiku da Gwamnonin G-5 Masu Yiwa PDP Barazana | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Wasu manyan Arewa ke son a sulhunta Atiku da su Wike

Majiya ta nuna cewa, shiga tsakani da IBB zai yi ya zo ne daga shawarin wasu manyan tsofaffin shugabannin soja daga yankin Arewacin Najeriya masu goyon bayan Atiku, Naija News ta tattaro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Har yanzu ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamonin G-5 da Atiku a yunkurinsu na ganin a tsige shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Iyochia Ayu tare da maye gurbinsa da dan Kudu.

Wannan rikici ya faro ne ta bangaren gwamna Wike, wanda ya sha kaye a zaben fidda gwanin da PDP ta gudanar a watannin baya da suka gabata.

Kara karanta wannan

Muna sane: IGP ya fadi matakin da 'yan sanda ke dauka bisa harin da aka kai kan tawagar Atiku

Maganganu da dama sun fito daga wadannan gwamnoni biyar masu adawa da Atiku, sun kuma ba da sharadin sulhu da dan takarar nasu na shugaban kasa.

G-5 ta kai ziyara jihar Bauchi

A makon nan ne gwamnoni G-5 suka dura jihar Bauchi a wata ziyara da suka kai don ganawa tare da tattauna da gwamna Bala Muhammad.

Majiyoyi sun bayyana cewa, ana kyautata zaton gwamnonin za su jawo Bala ne cikinsu a ci gaba da adawa da dan takarar shugaban kasan PDP Atiku Abubakar.

Jam'iyyar PDP na fuskantar kalubale tun bayan kammala zaben fidda gwanin da ya fito da Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.