Wike, Ortom da Wasu Abokansu Sun Dura Bauchi Domin Jawo Gwamna Tsaginsu

Wike, Ortom da Wasu Abokansu Sun Dura Bauchi Domin Jawo Gwamna Tsaginsu

  • Gwamnonin PDP masu adawa da dan takararsu na shugaban kasa sun dura jihar Bauchi don ganawa da gwamna Bala Muhammad
  • Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, gwamnoni hudu da suka dura jihar a yau za su yi kokarin jawo gwmamnan Bauchi cikinsu ne
  • Atiku na shan fama da wasu gwamnoni biyar da ke neman PDP ta tsige shugabanta kafin su goyi bayansa a zaben 2023 mai zuwa badi

Jihar Bauchi - Gwamnonin G-5 da suka yi kaurin suna wurin adawa da tafiyar Atiku, sun dura jihar Bauchi domin kokari jawo gwamna Bala Muhammad na jihar zuwa cikinsu.

Gwamnonin sun hada da Nyesom Wike na jihar Ribas, Samuel Ortom na jihar Benue, Okezie Ikpeazu na jihar Abia da Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, inji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Rikcin PDP: Gwamnonin G5 Sun Yi Wa Ayu Izgili A Yayin Da Ortom Ya Nada Wa Hanyar Zuwa Gidan Shugaban PDP Sunan Wike

Rahotanni sun bayyana cewa, tawagar G-5 na kokarin kambama wutar rikici ce da ta barke tsakanin dan takarar shugaban kas ana PDP Atiku Abubakar da gwamna Bala na Bauchi.

An ce sun iso gidan gwamnatin jihar Bauchi da misalign karfe 12:30 na rana ba tare da gwamna Seyi Makinde ba, wanda shi ma dan tawagar ne.

Gwamnonin G-5 sun ziyarci gwamnan Bauchi
Wike, Ortom da Wasu Abokansu Sun Dura Bauchi Domin Jawo Gwamna Tsaginsu | Hoto: Leadership News
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnonin G-5 na ta bayyana koke da neman a tsige shugaban PDP na nasa, Sanata Iyorchia Ayu daga kujerarsa, sharadin da suka bayar na goyon bayan Atiku a zaben 2023.

Rikicin Atiku da Bala Muhammad

Bala Muhamamd ya tado da sabon batu yayin da ya yi korafi ga Ayu cewa, Atiku yam ai dashi saniyar ware kuma bai ziyarce shi tun bayan da ya lashe zaen fidda gwani duk da ya ziyarci wasu da dama.

Gwamnan na Bauchi, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban majalisar kamfen Atiku a Arewa maso Gabas, ya kuma bayyana fushi kan yadda Atiku ya zabi kodinetocin kamfen daga Bauchi ba tare da yin shawari dashi ba.

Kara karanta wannan

Gudun Kada Ta Baci: An Yi Zaman Sulhu Tsakanin Atiku Da Kauran Bauchi

A wasikarsa ga Ayu, Bala ya bayyana irin bacin ran da ya shiga daga abubuwan da Atiku ya yi, kana ya nemi dan takarar shugaban kasan y aba shi hakuri.

Jaridar Leadership ta yada hotunan lokacin da wadannan jiga-jigai na PDP suka sauka a jirgi kuma gwamna ya tarbe su.

Gwamnonin G-5 sun yiwa Ayu izgili

Yayin da gwamna Samuel Ortom ya kaddamar da wasu ayyuka a jiharsa, gwamnonin G-5 sun halarci taron don nuna aminta da ke tsakaninsu.

A lokacin taron ne suka yiwa shugaban PDP, Iyochia Ayu izgili, tare da jaddada bukatar a tsige shi.

PDP dai na kara dulmusyewa cikin tabon rikici tun bayan kammala zaben fidda gwanin shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel