Yayin da Yake Kasar Waje, Buhari Ya yi Hasashen Yadda Zaben 2023 Zai Kasance
- Muhammadu Buhari ya yi hira da ‘yan jarida daga Birtaniya, ya yi magana a kan wanda zai gaje shi
- Shugaban Najeriyan yana ganin ‘Dan takaran jam’iyyar APC, Bola Tinubu ne za iyi nasara a zaben badi
- Buhari yace Tinubu fitaccen ‘dan siyasa ne wanda ya yi suna, kuma ya yi aiki a lokacin da ya yi Gwamna
United Kingdom - Mai girma Muhammadu Buhari ya yi bayanin abin da ya sa Asiwaju Bola Tinubu zai yi nasara a zaben shugaban kasa da za ayi.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi magana da gidan talabijin kasa na NTA yayin da yake kasar Birtaniya, inda ya je a duba lafiyar jikinsa.
Da aka tattauna da shi a ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamba 2022, Muhammadu Buhari yayi hasashen nasarar jam’iyyarsa ta APC ne a zaben 2023.
Shugaban kasar yake cewa Asiwaju Bola Tinubu zai lashe zaben shugabancin kasa saboda irin rawar da ya taka a lokacin da ya rike gwamna a Legas.
Tinubu ya bar ayyukan a-zo-a gani
Buhari ya shaidawa gidan talabijin cewa har yau ayyuka da nasarorin da Bola Tinubu ya samu daga shekarar 1999 zuwa 2007 a Legas suna nan har yau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A hirar da aka yi da shi, The Nation tace shugaban Najeriyan ya bayyana ‘dan takaran kujerar shugaban kasar a matsayin gawurtaccen ‘dan siyasa.
Babu murdiya a zaben 2023
Haka zalika shugaban kasar ya tabbatar da za ayi zaben adalci da gaskiya a shekara mai zuwa, yace zai so ya kafa wannan tarihin a kan gadon mulki.
A cewarsa, zai yi duk abin da zai iya wajen ya hana a shigo da kudi daga kasashen ketare domin ayi amfani da su wajen murde zabin da jama’a suka yi.
A nan ne ya yi magana a kan nasarar APC mai mulki a karo na biyu, yace jam’iyyarsa za ta kafa gwamnati bayan shudewar wa’adinsa a watan Mayun badi.
APC tayi sa'a da Tinubu - Buhari
“Za mu lashe zaben nan, ‘dan takaran shugaban kasar, Bola Tinubu sanannen ‘dan siyasa ne sosai a Najeriya.
Shi Tinubu ya yi gwamna sau biyu a jiharsa ta Legas, jihar da ta fi kowace kudi da yawan samun masu ziyara.
Saboda haka ina tunanin jam’iyyar (APC) tayi sa’a da ya yarda ya zama ‘dan takaranta na zaben shugaban kasa."
- Muhammadu Buhari
Ina ma Umahi aka ba tikiti - Kwankwaso
Amma a gefe guda, sai aka ji Rabiu Musa Kwankwaso ya bude ofishin Kamfen jam’iyyar NNPP a Ebonyi, har ya soki zabin APC na ‘dan takarar shugaban kasa.
Kwankwaso ya nuna an yi kuskure wajen tsaida Bola Tinubu, sannan yace gwamna David Umahi ya tafka kuskure da ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng